Bayan Ba da Hakuri, Tinubu Ya Kara Daukan Matakin Dakile Zanga Zangar Matasa

Bayan Ba da Hakuri, Tinubu Ya Kara Daukan Matakin Dakile Zanga Zangar Matasa

  • Gwamnatin tarayya ta kara daukan mataki domin ganin matasa ba su fita zanga zanga a ranar 1 ga watan Agusta ba
  • A yau Laraba ne ake sa ran dukkan yan majalisar zartarwa ta kasa za su zauna domin ganin an dakatar da fita zanga zangar
  • Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya ba yan Najeriya hakuri kan fita zanga zangar a jiya Talata

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta kara daukan mataki domin ganin matasa ba su fita zanga zanga ba.

Rahotanni sun nuna cewa sakataren gwamnatin tarayya ne ya fito da sabuwar hanyar da gwamnatin za ta nemi mafita a cikinta.

Kara karanta wannan

Wasu matasan Arewa sun fadi sharuda 3 kafin janye zanga zangar da aka shirya

Bola Tinubu
Gwamnatin tarayya ta dauki sabon matakin hana zanga zanga. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa a yau Laraba ake sa ran yan majalisar zartarwa za su zauna domin tattaunawa kan zanga zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin da Bola Tinubu ya fara dauka

A karon farko, shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga matasa kan cewa su hakura da zanga zangar da suke shirin yi.

A jiya Talata ne Bola Tinubu ya yi kira ga matasan kan cewa su jira su ga matakin da zai dauka kan matsalolin da suka ambata.

Sabon matakin da gwamnatin Tinubu ta dauka

Bayan kiran da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi, sakataren gwamnatin tarayya zai tara dukkan yan majalisar zartarwa domin daukan mataki na gaba.

Rahoton Daily Post ya nuna cewa ministocin Tinubu za su zauna domin ganin sun samu nasarar shawo kan matasan Najeriya.

Yaushe ministocin za su zauna?

Kara karanta wannan

Bayan gyaran kananan hukumomi, Tinubu ya dauko canza fasali ga aikin yan sanda

Rahotanni sun nuna cewa a yau Laraba, 24 ga watan Yuli dukkan ministocin za su zauna a ofishin sakataren gwamnatin tarayya.

Haka zalika sanarwar ta nuna cewa wajibi ne ga dukkansu su halarci zaman da misalin karfe 10 na safe.

An ba Tinubu mafita kan zanga zanga

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da matasa ke shirin zanga-zanga a wata mai kamawa, Ali Ndume ya bai wa shugaban Bola Tinubu mafita.

Sanata Ndume mai wakiltar Kudancin Borno ya bukaci Tinubu ya kira masu shirya zanga-zangar su zauna a teburin sulhu da gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng