Peter Obi Ya Yi Barazanar Maka Hadimin Tinubu a Kotu, Ya Fadi Dalilin Neman Diyyar N5bn
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi wa hadimin shugaban ƙasa barazanar maka shi a kotu
- Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayar da wa'adin sa'o'i 72 ga Bayo Onanuga domin ya fito ya nemi afuwa ko kuma su haɗu a gaban kotu
- Lauyan Peter Obi ya ce kalaman Onanuga na cewa shi ke kitsa zanga-zangar yunwa da aka shirya yi kan gwamnatin Tinubu ɓata suna ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Peter Obi ya ba mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, wa’adin sa’o’i 72 domin ya ba shi haƙuri.
Peter Obi ya ba shi wannan wa'adin ne saboda alaƙanta shi da ya yi da zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar nan.
Wace buƙata Peter Obi ya nema?
Lauyan Peter Obi, Alex Ejesieme, ya bukaci Bayo Onanuga ya nemi afuwa a manyan jaridu huɗu na ƙasa da kuma a shafinsa na sada zumunta, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya kuma buƙaci Bayo Onanuga ya biya shi N5bn saboda ɓata masa suna.
Ya yi barazanar shigar da ƙara kan ɓata sunan Peter Obi idan har wa'adin ya cika bai yi hakan ba, rahoton jaridar The Cable ya tabbatar.
Meyasa Peter Obi ya yi barazana zuwa kotu?
Onanuga ya yi zargin cewa magoya bayan Peter Obi na shirin tayar da zaune tsaye a Najeriya.
Lauyan Peter Obi ya bayyana zargin a matsayin wani “makirci ne da aka ƙirƙira” domin wulaƙantawa tare da kunyata wanda yake karewa.
Lauyan ya jaddada cewa Peter Obi ya kyamaci tashin hankali kuma a kodayaushe yana bin hanyoyin da doka ta tanada domin nuna rashin gamsuwarsa da wasu tsare-tsaren gwamnati.
Peter Obi ya caccaki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi ya caccaki yadda Shugaba Bola Tinubu ke nuna halin ko-in-kula kan halin ƙuncin da talakan Najeriya ke ciki.
Peter Obi ya ce kamata ya yi Shugaba Tinubu ya mayar da hankali kan yadda ƙasar nan za ta fita daga halin da take ciki ba wai nuna cewa ba talakawan Najeriya ba ne kadai ke cikin wahala ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng