Ana Fargabar Tarzoma, Gwamnan PDP Ya Fitar da Sanarwa Gabanin Zanga Zanga
- Gwamnatin jihar Bauchi karkashin Sanata Bala Muhammad ta fara shiri yayin da matasa ke yunkurin fara zanga zanga a Najeriya
- Ma'aikatar lafiya a jihar Bauchi ta yi bayani kan yadda za ta fuskanci ranar zanga zangar da matasan Najeriya ke shirin farawa
- A ranar 1 ga watan Agusta ne ake sa ran fara zanga zangar kawo karshen tsadar rayuwa a Najeriya da al'umma ke fama da ita
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta dauki mataki kan asibitoci da ma'aikatan lafiya yayin da ake shirin fara zanga zanga.
Shugaban dakunan shan magani, Dakta Rilwanu Mohammed ne ya fadi matakin da za su dauka da zarar an fara zanga zangar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ma'aikatar lafiya a jihar ta dauki matakin ne bayan ta samu bayanan sirri daga jami'an tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zanga zanga: Za a rufe asibitocin Bauchi
Shugaban dakunan shan magani a jihar Bauchi, Dakta Rilwanu Mohammed ya bayyana cewa za a rufe dukkan kananan asibitoci a jihar da zarar matasa sun fara zanga zanga a ranar 1 ga watan Agusta.
Dakta Rilwanu Mohammed ya ce sun dauki matakin ne biyo bayan samun bayanai kan cewa za a iya lalata asibitocin a lokacin zanga zangar.
Bauchi: Ma'ikatan lafiya za su zauna a gida
Haka zalika Dakta Rilwanu Mohammed ya bayyana cewa ma'aikatan lafiya a dukkan asibitocin jihar ba za su je aiki ba.
Rahoton Daily Post ya nuna cewa an dauki matakin ne domin kare lafiyar ma'ikatan daga kawo musu hari ko cutar da su a lokacin zanga zangar.
Yaushe za a bude asibitoci a Bauchi?
Dakta Rilwanu Mohammed ya bayyana cewa asibitocin za su cigaba da zama a kulle har sai an kammala zanga zangar.
Ya kuma kara da cewa duk da za su kulle asibitocin sun ba jami'an tsaro umurnin saka ido a kan su saboda kaucewa barnar bata gari.
Matakin na nuna cewa gwamnatin tana kan shiri kuma ba ta dauki lamarin zanga zangar matasan da wasa ba.
An raba kayan noma a Bauchi
A wani rahoton, kun ji cewa yayin da damina ta kankama Gwamna Bala Mohammed ya kaddamar da shirin tallafawa manoma a jihar Bauchi.
Gwamnan ya bayyana cewa shirin zai sayar da takin zamani a kan N20,000 kuma zai samar da sauran kayayyakin noma a farashi mai sauƙi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng