Ministan Tinubu Ya Dauki Zafi Kan Zanga Zanga, Ya Fadi Dalilin Shiryata

Ministan Tinubu Ya Dauki Zafi Kan Zanga Zanga, Ya Fadi Dalilin Shiryata

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya soki shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan a Agusta
  • Yayin da yake duba hanyar Apo-Karshi da ke Abuja, Wike ya buƙaci ƴan Najeriya da su yi haƙuri, su ƙarawa gwamnati lokaci
  • Ya kuma tabbatarwa jama’a cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana aiki tukuru domin kawo romon dimokuraɗiyya ga ƴan ƙasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, a ranar Talata, 23 ga watan Yuli, ya nuna rashin jin dadinsa game da shirin gudanar da zanga-zangar a faɗin ƙasar nan.

Wike ya bayyana zanga-zangar da aka shirya yi a watan Agusta a matsayin wacce za a yi saboda siyasa.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi barazanar maka hadimin Tinubu a kotu, ya fadi dalilin neman diyyar N5bn

Wike ya yi magana kan zanga-zangar adawa da Tinubu
Nyesom Wike ya ce akwai siyasa a shirin yin zanga-zanga kan gwamnatin Tinubu Hoto: @govwike
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne dai yayin da yake duba aikin hanyar Apo-Karshi, a babban birnin tarayya Abuja, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya ba ƴan Najeriya haƙurin zanga-zanga

Ministan na babban birnin tarayya Abuja ya bukaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri, yana mai cewa mutane da dama sun fi son sha yanzu magani yanzu, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tana aiki tuƙuru domin ganin ƴan Najeriya sun samu cin moriyar romon dimokuraɗiyya cikin gaggawa.

Wike ya bayyana cewa tun lokacin da Tinubu ya hau kan karagar mulki, ƴan Najeriya sun ga sauye-sauye masu kyau a harkokin mulki.

"Zanga-zangar da aka shirya siyasa ce kawai ba komai ba. Ya kamata mu yi haƙuri da wannan gwamnati."

Kara karanta wannan

APC ta fallasa masu shirya zanga zangar adawa da gwamnatin Tinubu

- Nyesom Wike

Karanta wasu labaran kan shirin zanga-zanga

Atiku ya magantu kan zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓukan 2019 da 2023, Atiku Abubakar, ya yi magana kan shirin zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan.

Atiku Abubakar ya bayyana cewa ƴancin ƴan ƙasa na yin zanga-zanga yana cikin kundin tsarin mulkin Najeriya kuma bai kamata a hana su shi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng