Shugaba Tinubu Ya Aike da Muhimmin Saƙo Ga Matasa Masu Shirin Yin Zanga Zanga
- Bola Ahmed Tinubu ya roƙi matasa su yayyafawa zuciyoyin su ruwan sanyi su janye shirinsu na yin zanga-zanga a wata mai kamawa
- Shugaban ƙasar ya buƙaci su kara masa lokaci domin magance dukkan abubuwan da suka dame su a ƙasar nan
- Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris ne ya bayyana haka a fadar shugaban kasa bayan ganawa da Tinubu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya roƙi matasan ƴan Najeriya su hakura su janye shirinsu na yin zanga-zanga kan ƙuncin rayuwa a wata mai zuwa.
Shugaban ya kuma tabbatarwa da wadanda suka shirya zanga-zangar cewa ya ji kokensu kuma yana bakin kokarinsa wajen ganin an magance duk wata damuwa da ta zame masu alaƙaƙai.
Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ne ya bayyana haka yayin hira da wasu ƴan jarida jim kaɗan bayan ganawa da Tinubu a Villa yau Talata, Channels tv ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya tura saƙo ga ƴan Najeriya?
Ya ce Shugaba Tinubu ya roƙi masu shirya wannan zanga-zanga mai taken, "kawo karshen gurbataccen shugabanci," su yi haƙuri su janye kudirinsu.
"Batun zanga-zangar da ake shirin yi, shugaban ƙasa ya ce babu bukatar yin hakan, ya roƙi (matasa) su yi hakuri su janye shirinsu, su dakaci matakin da gwamnatin za ta ɗauka kan damuwarsu."
"Ya kamata matasa su saurari shugaban ƙasa, su ƙara ba shi lokaci domin ganin tarin abubuwan alherin da ya shirya masu."
- Mohammed Idris.
Wasu matakai Tinubu ya fara ɗauka?
Dangane da matakan da Tinubu ke ɗauka domin yaye wa ƴan Najeriya kuncin rayuwa, ministan ya ce tuni gwamnatin tarayya ta baiwa jihohi hatsi da buhunan shinkafa.
Ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tura kayan tallafi zuwa jihohi domin a rabawa ƴan Najeriya da nufin magance yunwa da kuncin rayuwar da ake ciki, Daily Trust ta ruwaito.
IGP ya gargaɗi masu shirin zanga-zanga
A wani rahoton kuma Sufeto-Janar na ƴan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya yi gargaɗi kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a ƙasar nan.
Kayode Egbetokun ya yi gargaɗin cewa ƴan sanda ba za su zura ido ba su bari a fake da zanga-zangar domin tayar da rikici.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng