Abacha: Iyalin Tsohon Shugaban Ƙasa Sun Yi Rashin Nasara, Kotu Ta Yi Hukunci Bayan Shekaru 9

Abacha: Iyalin Tsohon Shugaban Ƙasa Sun Yi Rashin Nasara, Kotu Ta Yi Hukunci Bayan Shekaru 9

  • Iyalan marigayi tsohon shugaban mulkin soja, Janar Sani Abacha sun yi rashin nasara a ƙarar da suka maka gwamnatin Najeriya
  • Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi fatali da ƙarar, ta kuma umarci su biya wani kamfani N500m kudin wahalar shari'a
  • Maryam Abacha da Muhammad Abacha suka shigar da ƙarar domin kwato kadarorin da suke zargin gwamnati ta ƙwace masu a Abuja

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta kori ƙarar da iyalan tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, marigayi Sani Abacha suka shigar gabanta.

Iyalan marigayin sun shigar da ƙarar ne suna ƙalubalantar matakin gwamnatin Najeriya na kwace masu kadarar Abacha a Maitama da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Yusuf Gagdi: Abubuwan sani dangane da dan majalisar da ya siyawa 'yarsa motar kusan N100m

Marigayi Janar Sani Abacha.
Iyalan marigayi Abacha sun yi rashin nasara a shari'ar kwace kadarori Hoto: Contributor
Asali: Getty Images

Matar Abacha, Maryam Abacha da babban ɗanta da ke raye, Muhammad Abacha suka shigar da ƙara gaban kotun, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa iyalin Abacha suka nufi kotu?

Sun yi zargin cewa gwamnati ta soke takardar shaidar mallaka mai lamba FCT/ABUKN 2478 ta gidansu da ke Plot 3119 da aka ba su ranar 25 ga Yuni 1993.

An ƙwace gidan a watan Fabrairu, 2006 lokacin Nasir El-Rufai yana matsayin ministan Abuja bayan shekaru kusan takwas da rasuwar Janar Abacha.

A ƙarar, iyalan tsohon shugaban sun roki kotu ta dawo masu da kadararsu da ke kusa da Osara a Maitama da kuma N500m a matsayin ladan ƙarfa-ƙarfar da aka yi masu.

Waɗanda suka tuhuma a shari'ar sun haɗa da ministan Abuja, hukumar raya birnin tarayya (FCDA), shugaban ƙasa da kamfanin Salamed Ventures Limited wanda ya mallaki wurin a yanzu.

Kara karanta wannan

Dan majalisar APC ya gwangwaje ɗiyarsa da kyautar dalleliyar SUV bayan gama sakandare

Kotu ta yanke hukunci bayan shekara 9

Da yake yanke hukunci a shari'ar, alkalin kotun Mai Shari'a Peter Lifu, ya ce karar da iyalan Abacha suka shigar shekaru tara da suka wuce ta sabawa doka.

Ya ce maƙasudin kawo karar wato ƙwace kadarar ya faru ne a watan Fabrairu, 2006 amma masu ƙarar sun shigar da ƙorafi ne a watan Mayu, 2015.

Alkalin ya bayyana cewa sun shigar da ƙarar bayan karewar wa'adin da doka ta tanada na ƙalubalantar matakin da jami'in gwamnatin tarayya ya ɗauka.

Mai shari'a Peter Lifu ya ce ƙwace kadarorin ya halatta saboda tauye alkawurran da aka ɗauka, ciki har da gina wurin ba tare da sahalewar mahukunta ba.

Kotun ta umurci iyalan Abacha da su biya kamfanin Salamed Ventures Limited Naira miliyan 500 a matsayin kudin ɗawainiyar ƙara, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Tinubu ya miƙa kudirin albashi ga majalisa

Kara karanta wannan

Zanga zangar adawa da Tinubu ta samu cikas bayan wasu matasan Arewa sun fice

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya aika kudirin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata na N70,000 ga majalisar wakilai ranar Talata, 23 ga watan Yuli.

Shugaban ƙasar ya buƙaci ƴan majalisar su gaggauta amincewa da kudirin sabon albashin domin aiwatar da shi a kan lokaci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262