Bayan Farmakar Ɗan Majalisar NNPP, An Kama Wani da Ake Zargi da Babban Laifi a Kano
- Jami'an tsaro sun kama wani hatsabin mai garkuwa da mutane a yankin ƙaramar hukumar Dawakin Kudu a jihar Kano
- Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin mutumin da sace mutane, bayan haka ya kashe su kana ya ɓinne su a cikin gidansa
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce a halin yanzu suna ci gaba da bincike kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano ta tabbatar da damƙe ƙasurgumin mai garkuwa da mutane wanda aka gano gawarwaki a gidansa.
Bayanai sun nuna ana zargin mutumin da sace mutane, kashe su da kuma binne su a cikin gidansa da ke ƙaramar hukumar Dawakin Kudu.
'Yan sandan Kano sun kama almajiri
A cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, wanda ake zargin Almajiri ne da ya zo karatu yankin daga baya ya shiga harkar garkuwa da mutane, Tribune Nigeria ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bayyana cewa wanda ake zargin ya yi garkuwa da wasu mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, wadanda jami’an tsaro suka gano gawarwakinsu a gidansa da ke Dawakin Kudu.
Kano: Wani mataki ƴan sanda suka ɗauka?
Da aka tuntubi jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da kama wanda ake zargin.
Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa a halin yanzu jami'an ƴan sanda sun fara gudanar da bincike kan lamarin domin gano duka masu hannu a wannan ɗanyen aiki.
A cewarsa, rundunar ƴan sanda ta kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin bayan tono gawarwaki a gidan mutamin.
Kakakin ƴan sandan ya ce duk da an kama wasu mutane kan lamarin, ƴan sanda na ci gaba da zurfafa bincike.
Yan bindiga sun kashe basarake a Taraba
A wani rahoton na daban, an ji yan bindiga sun kai farmaki kan titin Takum zuwa Chanchangi, sun halaka basarake da ɗansa a jihar Taraba
Gwamna Agbu Kefas ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da kakakinsa ya fitar, ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalansa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng