Tinubu Ya Cika Alkawari, Buhunan Shinkafa Sun Fara Isa, Kano da Jihohi 21 Na Jiran Tsammani

Tinubu Ya Cika Alkawari, Buhunan Shinkafa Sun Fara Isa, Kano da Jihohi 21 Na Jiran Tsammani

  • A makon da ya wuce ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin raba tirelolin shinkafa ga dukkan jihohin Najeriya
  • Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin tirelolin shinkafa 740 domin kawo sauki kan tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya
  • Rahotanni sun nuna bayan mako guda har yanzu jihohi da dama ba su ga shinkafar ba wasu kuma sun samu har da garin kwaki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT Abuja - A makon da ya wuce gwamnatin tarayya ta yi alkawarin fara raba shinkafa ga al'ummar Najeriya.

Gwamnatin ta fara ƙoƙarin ne domin kawar da tsadar rayuwa wacce ke shirin haifar da zanga zanga a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana saura kwana 10 ayi zanga zanga, Tinubu ya dawo Najeriya bayan kammala taron AU

Raba tallafin abinci
Tallafin shinkafar Tinubu ya fara isa jihohi. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa a halin yanzu jihohi kadan ne a Najeriya suka samu shinkafar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihohin da suka samu shinkafar Tinubu

Rahotanni sun nuna cewa a halin yanzu jihohi biyar ne suka fara samun tallafin shinkafar cikin jihohi 36 da ke Najeriya.

Jihohi da suka samu shinkafar sun hada da jihar Anambara, Akwa Ibom, Bayelsa, Kwara da Rivers.

Irin

Yaushe za a fara raba shinkafar?

Daraktan hukumar SEMA a jihar Anambara, Paul Odenigo ya tabbatar da cewa sun samu shinkafa tirela 20.

Sai dai ya ce suna jiran karin bayani daga gwamnati kafin su dauki matakin fara raba shinkafar ga al'umma.

An samu garin kwaki a kason Rivers

Haka zalika gwamnatin jihar Rivers ta bayyana cewa ta samu buhuna 21,650 daga fadar shugaban kasa.

Sakataren gwamnatin jihar, Dakta Tammy Danagogo ya tabbatar da cewa sun samu tallafin buhunan hatsi 17,970 da buhunan garin kwaki 3,680.

Kara karanta wannan

"Ba mu bukatar shikafarka": Malamin Musulunci ya nemi bukata 1 wurin Tinubu

Dalibai sun rasu wajen raba tallafi

A wani rahoton, kun ji cewa dalibai da dama sun mutu a wurin da gwamnatin Nasarawa ta shirya rabon tallafin abinci ga ɗaliban jami'ar jihar.

Rahoto ya nuna cewa tun da asubahin ranar rabon ɗaliban suka mamaye wurin da aka shirya rabon, suka kutsa cikin rumbun ajiyar da tsiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng