Bayan An Karrama Shi, Farfesa Wole Soyinka Ya Fadi Abin da Zai Yi a Kan Gwamnatin Tinubu
- Fitaccen marubuci, Wole Soyinka ya bayyana cewa ba zai ce komai a kan yadda gwamnatin Bola Tinubu ke tafiya ba
- Wannan na zuwa bayan ya yi alkawarin cewa zai tofa albarkacin bakinsa kan salon mulkin Bola Ahmed Tinubu idan ya shekara
- Amma a zantawarsa da manema labarai, marubucin ya ce zai ba marada kunya ta hanyar yin gum da bakinsa duk da ana jira ya ce wani abu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Shahararren marubuci, Farfesa Wole Soyinka ya bayyana cewa ba zai ce komai a kan salon mulkin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta karrama shi da ta hanyar mayar da sunan shi a babban dakin taro na kasa da ke Abuja.
Jaridar PM News ta wallafa cewa Farfesa Soyinka ya bayyana ra'ayinsa ne yayin amsa tambayoyi a bikin cikarsa shekara 90 da haihuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wole Soyinka ya ki cika alkawarinsa
A shekarar 2023, Farfesa Wole Soyinka ya bayyana cewa nan gaba kadan zai magantu kan yadda gwamnati ke gudanar da mulki a kasar nan, The Cable ta wallafa.
Shahararren marubucin ya bayyana cewa zai tofa albarkacin bakinsa kan yadda ake gudanar da akalar gwamnati idan Tinubu ya cika shekara guda a kan mulki.
Amma a zantawarsa da manema labarai, Wole Soyinka ya ce ya san jama'ar Najeriya na jiransa ya ce wani abu a kan mulkin Tinubu saboda kawai a ce ya ce wani abu.
Tinubu: "Zan ba marada kunya" Soyinka
Farfesa Wole Soyinka ya ce ba zai ce komai a kan yadda gwamnatin Tinubu ke gudana ba saboda ya ba wa mara da kunya.
Ya ce saboda kawai ya ce zai yi magana ba ya nufin zai ce komai ana cika shekara guda da sabuwar gwamnatin kasar nan.
Tinubu ya karrama Wole Soyinka
A baya mun kawo labarin cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta karrama ta hanyar sanya sunansa a titin N20 da ya taso daga 'Northern Parkway' zuwa arewacin Abuja.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya karrama Wole Soyinka ne saboda yadda ya jawo wa Najeriya mutunci da farin jini a idon duniya ta hanyar aikinsa na rubuce-rubuce.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng