“Kowa a Fusace Ya Ke”: NLC Ta Ba Tinubu Mafita Kan Shirin Zanga Zanga
- Shugaban kungiyar NLC a Najeriya, Joe Ajaero ya bayyana damuwa kan halin kunci da ake ciki inda ya ce kowa a fusace ya ke
- Ajaero ya kawo hanya mafi sauki domin dakile shirin zanga-zanga a Najeriya ga Shugaba Bola Tinubu domin kiyayewa
- Wannan na zuwa ne yayin da ake shirin fita zanga-zanga a fadin kasar domin nuna rashin jin dadi kan halin da ake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kungiyar Kwadago a Najeriya ta ba Shugaba Bola Tinubu shawarar yadda zai dakile shirin zanga-zanga a kasar.
Kungiyar ta ce hanya daya mafi dacewa wurin dakile zanga-zangar ita ce tattaunawa da fusatattun matasan.
NLC ta ba Tinubu shawara kan zanga-zanga
Shugaban kungiyar, Joe Ajaero shi ya bayyana haka a jiya Litinin 22 ga watan Yulin 2024, kamar yadda Tribune ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ajaero ya ce zanga-zanga 'yanci ce ta 'yan kasa inda ya ce miliyoyin 'yan Najeriya sun fusata kan halin kunci da ake ciki a fadin kasar.
Ya ce mafi yawan iyalai a Najeriya ba su iya samun cin abinci sau biyu a rana yayin da suke rayuwa cikin kunci da talauci, cewar Channels TV.
Zanga-zanga: NLC ta kawo mafita ga Tinubu
"Yayin da ake kara kusantar ranar zanga-zanga, kungiyar NLC ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya gayyaci shugabannin masu zanga-zangar."
"Ana cikin mawuyacin hali, kowa a fusace ya ke a Najeriya wanda lokaci ne da ya kamata gwamnati ta tattauna ba yakar 'yan kasa ba."
"Maganar gaskiya ita ce ba za ka mauje yaro ba kuma a lokaci guda ka ce za ka hana shi kuka, ya kamata a dauk matakin da ya ce a daidai wannan lokaci."
- Joe Ajaero
Matasan Arewa sun janye daga zanga-zanga
A wani labarin, kun ji cewa wata kungiyar matasa ta janye daga zanga-zanga yayin da ake ci gaba shirye-shiryen fitowa a kasar.
Gamayyar kungiyoyin matasan suka ce sun tsame hannunsu a zanga-zangar inda suka zargi wasu na kokarin amfani da hakan wurin kawo rigima.
Shugaban kungiyar, Kwamred Murtala Garba ya ce suna zargin wasu mutane sun shirya kwace ikon zanga-zangar tare da kawo tsaiko a yankin Arewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng