Bello Turji: Gwamnatin Zamfara Ta Yi Martani Ga Ministan Tsaro, Matawalle Bayan Ba Ta Shawara
- Gwamnatin jihar Zamfara ta mayar da martani ga karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle kan maganganunsa game da tsaro
- Gwamnatin jihar ta bayyana himmatuwarta wurin tabbatar da kawo karshen rashin tsaro ba tare da yin sulhu da su ba
- Wannan ce-ce-ku-ce na zuwa ne bayan faifan bidiyon dan ta'adda, Bello Turji inda ya ke zargin Matawalle kan ta'addanci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Yayin da Bello Turji a wallafa faifan bidiyo kan ta'addanci, an fara musayar yawu tsakanin gwamnatin Zamfara da Bello Matawalle.
Gwamnatin jihar ta tabbatar da cewa babu abin da zai saka ta zaman tattaunawa da 'yan bindiga saboda ba shi ne mafita ba.
Gwamnatin Zamfara ta caccaki Bello Matawalle
Hadimin Gwamna Dauda Lawal a bangaren sadarwa, Alhaji Faruk Ahmad shi ya tabbaar da haka a birnin Gusau, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Faruk ya bayyana haka ne yayin martani ga kalaman tsohon gwamnan jihar kuma karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle.
Ya ce Gwamna Lawal yana iya bakin kokarinsa wurin kawo karshen hare-haren 'yan bindiga a jihar domin tabbatar da zaman lafiya.
Har ila yau, Ahmad ya ce Gwamna Lawal a shirye ya ke da hada kai da duk wani mai neman kawo karshen 'yan bindiga a jihar.
"Mun godewa Allah yanzu 'yan bindiga na bayyana masu daukar nauyinsu, gwamnati mai ci tana kokarin daukar matakai da suke haifar da 'da mai ido."
"Ina mai tabbatar muku da cewa gwamnatin Zamfara ba za ta yi sulhu da 'yan bindiga ba, za ta ci gaba da yakarsu, wadanda suke son mika wuya su yi."
- Faruk Ahmad
Matawalle ya ba gwamnatin Zamfara shawara
Wannan ce-ce-ku-ce na zuwa ne bayan dan ta'adda, Bello Turji ya fito karara inda ya ke zargin Matawalle da hannu a ta'addanci.
Sai dai Matawalle ya yi martani inda ya karyata zargin yayin da ya ce an yi haka ne domin bata masa suna.
Matawalle ya shawarci gwamnan da cewa ya yi amfani da kudin da ya ke kashewa wurin bata masa suna domin dakile matsalar tsaron jihar Zamfara.
Bello Turji ya zargi Matawalla da ta'a'ddanci
Kun ji labari cewa dan ta'a'dda, Bello Turji ya sake bidiyo inda ya ke zargin karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle kan ta'addanci a Zamfara.
Turji ya ce yana da hujjoji masu karfi kan zargin da ya ke yi inda ya ce Matawallae ne ya sake lalata harkokin tsaron jihar gaba daya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng