Yaki Zai Dauki Zafi, Sojoji Sun Bankado Babban Abin da Ya Kawo 'Yan Bindiga Arewa

Yaki Zai Dauki Zafi, Sojoji Sun Bankado Babban Abin da Ya Kawo 'Yan Bindiga Arewa

  • Rundunar sojin Najeriya ta bayyana matsalolin da suka dabaibaye harkokin tsaro a yankin Arewa maso yammacin Najeriya
  • Hafsun sojojin Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ne ya bayyana matsalolin a wani taron jami'an tsaro a birnin tarayya Abuja
  • Rundunar sojin ta bayyana yadda ayyukan yan ta'adda ke jefa al'ummar yankin cikin mawuyacin halin rayuwa da asarar rayuka

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta yi bayani kan harkokin tsaro a Arewa maso yammacin Najeriya.

Shugaban hafsun sojojin Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya bayyana abubuwan da ke kawo cikas kan yaki da yan ta'adda a yankin.

Sojojin Najeriya
Sojoji sun yi taro domin magance matsalar tsaron Arewa maso yamma. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito rundunar sojin ta fadi haka ne a wani taron horo ga kwamandojin da suke jagorantar yaki a Arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Bayan Ali Ndume, Sanata ya kara cire tsoro ya fadawa Tinubu gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun fadi silar rashin tsaron Arewa

Hafsun sojojin Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya ayyana ayyukan haƙar ma'adanai ta haramtacciyar hanya cikin abin da ke ta'azzara matsalar tsaro.

Ya kara da cewa daga cikin abubuwan akwai satar shanu da satar mutane da dai sauran munanan ayyuka.

Matakin da sojoji za su dauka

Wanda ya wakilci Hafsun sojojin, Manjo Janar Benson Sijen ya bayyana cewa dole sai sojoji sun sake shiri kan yaki da yan ta'adda a yankin.

Manjo Janar Benson Sijen ya kara da cewa akwai buƙatar sojoji su kasance suna zaune kan shiri sama da yadda yan bindigar ke kwana cikin shiri.

Barnar da yan ta'adda ke yi a Arewa

Rahoton PM News ya nuna cewa Manjo Janar Benson Sijen ya bayyana cewa barnar da yan ta'addan ke yi na jawo asarar rayuka da dukiyoyi a Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ta yi babbar barna a jihar Arewa, mutum 1,664 sun rasa matsugunni

Saboda haka ya ce aka fara ba da horo ga kwamandojin domin kawar da yan ta'addar a yankin da ke samar da abinci sosai a Najeriya.

An kashe babban soja a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa jami'in gudanarwa a rundunar sojojin Operation Save Haven, Christopher Luka ya rasa ransa a jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiya.

An tattaro cewa jami'in hukumar shige da ficen wanda ke aiki da rundunar ya mutu ne lokacin da ya jagoranci sojoji domin kwato shanu a Barkin Ladi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng