'Yan Bindiga Sun Hallaka Babban Jami'in Dan Sanda da Wasu Mutum 3

'Yan Bindiga Sun Hallaka Babban Jami'in Dan Sanda da Wasu Mutum 3

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari kan jami'an ƴan sanda da ke gudanar da aikin sintiri a garin Aba na jihar Abia
  • Ƴan bindigan waɗanda suka buɗewa jami'an tsaron wuta inda suka hallaka wani Sufeton ƴan sanda tare da wasu mutum uku
  • Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin ta ce jami'an sun hallaka mutum biyu daga cikin ƴan bindigan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abia - Wasu ƴan bindiga sun kashe wani Sufeton ƴan sanda mai suna Shehu Oyibo, da wasu mutane uku a jihar Abia.

Ƴan bindigan sun kai harin ne lokacin da jami'an ƴan sandan ke aikin sintiri a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wanda ake zargi da 'kitsa' kisan janar na sojoji a Kano

'Yan bindiga sun kai hari a jihar Abia
'Yan bindiga sun hallaka dan sanda a jihar Abia Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta kawo rahoto cewa lamarin ya auku ne a kan hanyar Ngwa cikin garin Aba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka farmaki ƴan sanda

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan jihar Abia, ta ce jami'an ƴan sandan sun hallaka mutum biyu daga cikin ƴan bindigan, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

Ta bayyana sauran mutum ukun da suka mutu a matsayin Chika Godliveth, Onyenaturuchi Jonah, da Eniobong Godsgift Clement. 

"A ranar 21 ga watan Yuli, 2024, da misalin ƙarfe 11:28 na safe, jami’an ƴan sanda da ke cikin tawagar RRS, a Aba, sun fuskanci hari daga wajen ƴan bindiga dake cikin wata mota mai ruwan toka ƙirar Sienna."
"An kai musus harin ne yayin da suke aikin sintiri a kan hanyar Ngwa kusa da kwanar masallaci. Ƴan bindigan sun buɗe wuta kan jami'an tsaron amma sun samu nasarar daƙile harin."

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan jami'in dan sanda ya bindige mahaifinsa har lahira

- Maureen Chinaka

Maureen Chinaka ta ƙara da cewa an ajiye gawarwakin mutanen da suka rasu a ɗakin ajiye gawa.

Gwamna ya shirya sulhu da ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Benue ta ce a shirye ta ke ta hau kan teburin sulhu da ƴan bindigan da ke kashe-kashe a jihar.

Gwamnatin ta shirya tattaunawa da ƴan bindiga a jihar ne domin fahimtar kokensu da nufin sanya su ajiye makamansu su daina kashe-kashe a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng