Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Karbar Harajin N425bn Daga Wajen Bankuna
- Gwamnatin tarayya za ta karɓi sabon haraji daga hannun wasu bankuna guda bakwai na ƙasar nan saboda ribar da suka samu
- Sabon harajin da gwamnatin za ta karɓa ya kai sama da N425bn saboda ribar da bankunan suka samu sakamakon ƙaruwar darajar kuɗaden waje a shekarar 2023
- Tuni majalisar dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na a yiwa kuɗirin dokar kuɗi gyara ta yadda gwamnati za ta iya karɓar harajin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta shirya ƙarɓar harajin sama da N425bn daga wajen wasu bankuna bakwai na ƙasar nan.
Harajin wanda sau ɗaya za a karɓe shi, ya shafi ribar da bankunan suka samu saboda ƙaruwar darajar kuɗaɗen ƙasashen waje a shekarar 2023.
Majalisa ta amince da buƙatar Tinubu
Jaridar The Punch ta ce a ranar Laraba, majalisar dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu na yin gyara ga ƙudirin dokar kuɗi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙasan dai ya buƙaci a yiwa dokar gyara ne domin ƙaƙaba harajin kan ribar da bankunan suka samu sakamakon cinikayyar kuɗaɗen ƙasashen waje a shekarar 2023.
Meyasa gwamnati za ta karɓi harajin?
Irin wannan harajin dai gwamnati na ƙaƙaba shi ne kan ɓangarorin kasuwanci waɗanda suka amfana sosai da wani yanayi na kasuwa.
Binciken da jaridar ta yi daga rahoton shekara-shekara na bankuna a kasuwar hada-hadar kuɗi, ya nuna cewa bankunan sun samu riba mai gwaɓi a shekarar 2023.
Bankunan da za a karbi haraji hannunsu
Bankunan guda bakwai sun samu ribar N851bn daga hada-hadar kuɗaɗen ƙasashen waje a shekarar 2023.
Bankunan guda bakwai sun haɗa da Guaranty Trust Holding Company, United Bank for Africa, Access Holdings, FCMB Group, FBNHoldings, Zenith Bank, da Fidelity Bank Plc.
Hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta ƙasa (FIRS) ce za ta tattara tare da karɓar harajin a wajen bankunan.
Bankunan suna da zaɓin su biya harajin ba a lokaci ɗaya ba, amma sai da amincewar hukumar ta FIRS.
Ministar Tinubu ta yi fallasa
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta yi zargin cewa akwai wasu shafaffu da mai a gwamnati da suka takura mata.
Ministar matar ta yi zargin cewa ana takura mata ne saboda ta ƙi sanya kan buƙatar karɓo bashin $500m daga bankin duniya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng