Rusau: Ba a Gama Rikicin Sarauta ba, Abba Ya Dawo da Zancen Ruguza Wasu Wurare a Kano

Rusau: Ba a Gama Rikicin Sarauta ba, Abba Ya Dawo da Zancen Ruguza Wasu Wurare a Kano

  • Yan kasuwa a jihar Kano da ke kan titin Jami'ar Bayero sun yi korafi kan kokarin ruguza musu wuraren sana'a da gwamnatin ta ke kokarin yi
  • Wani dan kasuwa, Ibrahim Mu'azzam ya bayyana halin da suke ƙoƙarin shiga da kuma yin kira ga gwamnatin Abba Kabir Yusuf kan lamarin
  • Duk da haka, kwamishinan tsare-tsaren birni na jihar Kano, Abduljabbar Umar ya yi karin haske kan halin da ake ciki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Yayin da gwamnatin Abba Kabir ta dauko magana kan rusau a hanyar jami'ar Bayero, yan kasuwa sun koka.

Yan kasuwar da rushe-rushen yake shirin shafa sun yi kira na musamman ga gwamnatin jihar domin tausaya musu.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Kungiyar Amnesty Intl ta caccaki gwamnati kan kama 'dan gwagwarmyan Tiktok

Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan ruguza wurare. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa kwamishinan tsare-tsaren birni na jihar Kano, Abduljabbar Umar ya bayyana halin da ake ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan kasuwan Kano sun koka da rusau

Wani dan kasuwa a titin BUK, Ibrahim Mu'azzam ya bayyana cewa saka alamar rusa musu wuraren ya zo musu da matukar mamaki.

Ibrahim Mu'azzam ya ce an sayar musu da wuraren shekaru da dama kuma su suka raya wuraren ta yadda masu barna suka kauracewa wajen.

Saboda haka ya roki gwamantin jihar da ta tausaya musu ta musu adalci kan cewa su masu goyon bayanta ne kuma sun yiwa gwamna adduo'i a lokacin da yake shari'a a kotu.

Rusau: Gwamnatin Kano ta yi martani

A bidiyon da Trust TV ta wallafa, kwamishinan tsare tsaren gari na jihar Kano, Abduljabbar Umar ya tabbatar da cewa su na sane da abin da yake faruwa a wajen.

Kara karanta wannan

Kano: Sarki Sanusi II ya koka kan halin kunci da ake ciki, ya yabawa gwamnatin Abba

Abduljabbar Umar ya bayyana cewa hakkin gwamantin jihar ne ta tabbata da garin na cikin tsarin da ya kamata musamman cikin birni.

Saboda haka ya ce sun samu kukan da mutanen suka shigar kuma za su yi bincike su fitar da sakamako nan kusa kadan domin kowa yasan matsayinsa.

Za a yi zaben kananan hukumomi a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta mutunta hukuncin kotun koli kan tabbatar wa kananan hukumomi 'yancin gashin kansu,

Darakta Janar kan yada labaran gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya kara da cewa gwamnati ta shirya gudanar da zaben kananan hukumomi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng