Hankula Sun Tashi Bayan Jami'in Dan Sanda Ya Bindige Mahaifinsa Har Lahira a Borno

Hankula Sun Tashi Bayan Jami'in Dan Sanda Ya Bindige Mahaifinsa Har Lahira a Borno

  • Wani jami'in ɗan sanda da ke aiki a jihar Borno ya zama silar raba mahaifinsa da duniya bayan ya buɗe masa wuta
  • Majiyoyi sun bayyana cewa jami'in ɗan sandan mai suna Sunday Wadzani, ya hallaka mahaifin na sa ne bayan wata ƴar taƙaddama ta ɓarke a tsakaninsu
  • Tuni aka cafke Sunday Wadzani wanda ake zargi da hallaka mahaifinsa wanda shi ma tsohon jami'in rundunar ƴan sandan Najeriya ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Wani jami'an ɗan sanda a jihar Borno mai suna Sunday Wadzani ya kashe mahaifinsa a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Lamarin ya faru ne a bayan hedikwatar ƴan sandan jihar da ke Modugannari, ranar Lahadi, 21 ga watan Yulin 2024.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun zo da sabon ta'addanci, sun yi barna a ofishin 'ƴan sanda

Dan sanda ya kashe mahaifinsa a Borno
Jami'in dan sanda ya hallaka mahaifinsa a Borno Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda ɗan sanda ya kashe mahaifinsa a Borno

Jaridar Daily Trust ta ce wanda ake zargin yana aiki ne a majalisar dokokin jihar Borno.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar wata majiyar tsaro, an kama Sunday Wadzani kuma a yanzu haka yana tsare a ofishin ƴan sanda a unguwar GRA.

Wani ɓangare na wata takarda da aka rubuta kan lamarin na cewa:

"Sajan na ƴan sanda mai suna Sunday Wadzani da ke aiki a jihar Borno a ranar 21 ga watan Yuli 2024 da misalin ƙarfe 4:20 na Yamma, ya harbe mahaifinsa Wadzani Ntasiri (mai ritaya) sau bakwai bayan wata ƴar ƙaramar hatsaniya a Maiduguri."

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Legit Hausa ta samu jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Kenneth Daso, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin.

ASP Daso ya tabbatar da cewa jami'an ƴan sanda da ke aikin sintiri sun isa wajen bayan sun ji ƙarar harbin bindiga, inda suka ƙwace bindigar daga hannunsa tare da tafiya da shi.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya tada hankalin duniya, ya fadi abin da zai faru idan bai ci zabe ba

Ya bayyana cewa jami'in yana tsare yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Ƴan sanda sun cafke Sufeto

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan Kogi ta tabbatar da cafke wani jami'inta, Sufeto Aminu Mohammed bisa zargin fashi da satar mota.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, SP Williams Ovye-Aya ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce tuni suka cika hannunsu da Sufeton da ake zargi da aikata laifin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng