Yayin da Dangote Ya Fara Samun Matsala a Kudu, Za a Fara Farfaɗo da Kamfanonin Arewa
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya fara motsawa kan farfaɗo da kamfanonin da ke yankin Arewa
- Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi bayani ne yayin da ya ziyarci kamfanin sarrafa takalma na zamani a jihar Borno
- Haka zalika gwamna Zulum ya bayyana yunkurin da yi na fara farfaɗo da kamfaninn samar da tumatur a jihar Borno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Yayin da matatar Dangote ke fuskantar barazana, gwamantin jihar Borno ta fara ƙoƙarin kawo cigaba ta fannin masana'antu a Arewa.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana kamfanin da jihar ke kokarin samarwa a halin yanzu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Farfesa Babagana Umara Zulum ya kuma kai ziyara kamfanin takalma a jihar Borno.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfaɗo da kamfanin tumatur a Borno
A yayin ziyarar ba zata da gwamna Zulum ya kai tsohon kamfanin tumatur a Borno yayi bayani yadda za a farfaɗo da shi.
Farfesa Zulum ya umurci a fara aikin zamanantar da na'urorin kamfanin nan take domin samar da damar yin aiki yadda ya kamata a kamfanin.
Haka zalika ya umurci a samar da filin nomar rani hekta biyar domin samar da wadataccen tumatur ga kamfanin wanda za a fadada shi zuwa hekta 100 nan gaba kadan.
An samar da kamfanin takalma a Borno
Haka zalika Farfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci kamfanin takalma na NIETEL Shoe and Tannery a jihar a cewar rahoton Arise News.
Yayin ziyarar, Gwamna Zulum ya tabbatar da cewa a yanzu haka kamfanin ya fara aiki domin samar da kaya da za a rika amfani da su.
Gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa an samu nasarar farfaɗo da kamfanin ne a karkashin hadaka tsakanin gwamnati da yan kasuwa.
Dangote zai sa matatarsa a kasuwa
A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya fara shirin siyar da matatar man fetur ɗinsa da aka kwashe shekaru ana ginawa a jihar Legas.
Attajirin wanda ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika ya ce a shirye yake ya siyar da matatar man fetur ɗin ga kamfanin NNPCL idan za su saye shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng