Dangote Ya Fadi Abin da Abokansa Ke Yi Masa Kan Matsalar da Yake Fuskanta Daga Gwamnati
- Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, na ci gaba da kokawa kan matsalolin da yake fuskanta kan matatar man fetur ɗinsa
- Hamshaƙin attajirin ya bayyana cewa wani daga cikin attajiran abokansa ya fara yi masa gori saboda matsalar da yake fuskanta daga wajen hukumomi
- Ya ce a shekarun bayan ya yi ƙoƙarin ba abokin nasa shawarar ya tsaya ya zuba hannun jari a Najeriya maimakon ƙasashen waje
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Hamshaƙin attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aliko Dangote, ya ce ɗaya daga cikin abokansa da ya fara zuba jari a ƙasashen waje ya fara yi masa gori.
Shugaban na rukunin kamfanonin Dangote ya ce abokin nasa na yi masa gori ne saboda matsalolin da yake fuskanta daga wajen gwamnati cikin ƴan kwanakin nan.
Dangote ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da jaridar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abokin Dangote ya fara yi masa dariya
A cikin hirar ya bayyana cewa shekara huɗu da suka wuce ya yi ƙoƙarin nunawa wani abokinsa cewa ya zuba hannun jari a Najeriya amma sai ya zaɓi ya tafi ya zuba a ƙasashen waje.
"Shekara huɗu da suka wuce, ɗaya daga cikin attajiran abokaina ya fara zuba hannun jari a ƙasar waje. Ban yarda da hakan ba sannan na roƙe shi da ya sake tunani saboda ƙasarsa."
"Ya ɗora alhakin matakin da ya ɗauka kan rashin tsare-tsare masu tabbas da waɗanda za su so ganin bayansa domin kare muradunsu."
"Yanzu wannan abokin na wa yana ta yi mani dariya cikin ƴan kwanakin nan, yana cewa sai da ya gargaɗe ni ga shi kuma ta tabbata ya yi gaskiya."
- Aliko Dangote
Dangote ya nuna cewa ya zuba kuɗadensa ne a matatar man fetur ɗin domin taimakawa wajen magance matsalar man fetur a Najeriya, inda ya yi mamakin yadda wasu mutane ke adawa da shi.
Karanta wasu labaran kan Dangote
- "Daga watan Yuni": An shiga murna yayin da Dangote ya yi albishir kan matsalar mai
- Gwamnati ta faɗi ainihin halin da matatar Dangote take ciki, ashe ba a yi rabin aiki ba
- Dangote ya musanta zargin samar da dizal mara inganci, ya kalubalanci hukumar NMDPRA
Dangote ya shirya siyar da matatarsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aliko Dangote ya ce a shirye yake ya sayar da matatar man fetur ɗinsa.
Dangote ya ce ya shirya sayar da matatar man fetur ɗin ta biliyoyin daloli ga kamfanin NNPC biyo bayan matsalolin da yake fuskanta daga mahukuntan gwamnati.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng