Masu Zanga Zangar Goyon Bayan Tinubu Sun Bullo, Za a Raba Kan Matasan Najeriya

Masu Zanga Zangar Goyon Bayan Tinubu Sun Bullo, Za a Raba Kan Matasan Najeriya

  • Gwamnonin Najeriya na cigaba da tura gargadi ga matasa kan shirin gudanar da zanga zangar yaki da tsadar rayuwa a fadin ƙasar
  • Gwamnatin Kogi ta shiga sahun jihohin da suka isar da sakon gargadi ga matasan Najeriya kan nisantar zanga zangar da ake shirin yi
  • Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo ya bayyana wani yunkuri da ake wajen ganin an fasa yin zanga zangar da ake shirin farawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kogi - Gwamantin jihar Kogi ta bi sahun wasu gwamnonin Najeriya wajen yaki da fita zanga zanga.

Gwamna Ahmed Usman Ododo ya ce babu dalilin da zai fitar da matasa zanga zanga a wannan lokacin da gwamnati ke kokari.

Kara karanta wannan

Zanga zangar adawa da Tinubu: Gwamnan Arewa ya fadi abin da matasan jiharsa za su yi

Gwamna Ododo
Gwamna Ododo ya gargadi masu zanga zanga. Hoto: Kingsley Femi Fanwo
Asali: Facebook

Kwamishinan yada labaran jihar Kogi, Kingsley Femi Fanwo ne ya fitar da sanarwar a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mabiya Tinubu za su yi zanga zanga

Gwamnatin Kogi ta bayyana cewa akwai labari mai karfi da suka samu na wasu matasa masu goyon bayan Tinubu da suke shirin fita zanga zanga domin mara masa baya.

Matasan za su fito zanga zanga ne domin zama kishiya ga masu shirin zanga zangar yaki da tsadar rayuwa da ake a gwamantin Bola Tinubu.

Ododo: 'Babu dalilin yin zanga zanga'

Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo ya bayyana cewa kasancewar gwamantin Tinubu tana kokarin magance matsalolin Najeriya bai kamata a fito zanga zanga ba.

Gwamna Ododo ya ce da a ce ba a wani kokari ne to da tabbas matasan su na da dalilin fitowa zanga zanga.

Gwamna ya yi kira kan zanga-zanga

Kara karanta wannan

Tarihi bai manta ba: Nasarori da matsalolin da aka samu lokutan zanga zanga a baya a Najeriya

Haka zalika gwamna Ododo ya ce ya kamata iyaye su ja kunnen ƴaƴansu dangane da fita zanga zangar, rahoton Daily Trust.

Ya fadi haka ne saboda akwai tunanin cewa ana so ayi amfani da zanga zangar ne wajen kawo fitina a Najeriya.

Zanga zanga: Matasan Kenya sun yi nasara

A wani rahoton, kun ji labari cewa babbar kotun kasar Kenya ta yanke hukunci a kan hana zanga zanga da rundunar yan sandan kasar ta yi a cikin makon da ya wuce.

Haka zalika bayan yanke hukuncin, babbar kotun ta ba rundunar yan sandan kasar Kenya sabon umurni da za ta aikata da gaggawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng