Rashin Tsaro: Gwamnan Arewa Ya Shirya Yin Sulhu da 'Yan Bindiga

Rashin Tsaro: Gwamnan Arewa Ya Shirya Yin Sulhu da 'Yan Bindiga

  • Gwamnatin Benue ta koka kan yadda ƴan bindiga ke ci gaba da cin karensu babu babbaka a jihar kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba
  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar ya ce gwamnatin a shirye take ta hau kan teburin sulhu da 'yan bindigan domin kawo ƙarshen kashe-kashen da suke yi
  • Ya koka kan yadda ƴan bindigan ba su zuwa idan gwamnati ta kira su domin ta saurari kokensu da nufin kawo ƙarshen ayyukansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Gwamnatin jihar Benue ta ce a shirye ta ke ta hau kan teburin sulhu da ƴan bindigan da ke kashe-kashe a jihar.

Gwamnatin ta shirya tattaunawa da ƴan bindiga a jihar ne domin fahimtar kokensu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka mutum 2, sun sace wasu matafiya 5 a wani hari

Gwamnatin Benue ta shirya sulhu da 'yan bindiga
Gwamnatin Benue ta bukaci 'yan bindiga sun ajiye makamansu Hoto: Hyacinth Iormem Alia
Asali: Facebook

Kwamishinan yaɗa labarai, al’adu da yawon buɗe ido, Mathew Abo, ya bayyana hakan a wata hira da jaridar The Punch a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta zargi ƴan bindiga a Benue

Kwamishinan ya zargi ƴan bindigan da rashin adalci ga gwamnatin Gwamna Hyacinth Alia na jihar.

Ya ce gwamnati ta sha gayyatar ƴan bindigan domin tattaunawa amma suna dagewa cewa sai gwamnan ya fara yi musu afuwa, yayin da suke ci gaba da kashe mutane.

Kwamishinan ya yi magana ne bayan a baya-bayan nan ƴan bindiga sun kashe mutum 18 a gundumar Mbache da ke ƙaramar hukumar Katsina-Ala.

Me gwamnatin ta ce kan sulhu da ƴan bindiga?

"Wani alƙawari ne gwamnan ya yi wa ƴan bindiga? Shin sun ajiye makamansu? Gwamna na cin zaɓe aka rantsar da shi suka fara kai hare-hare. Ba a yin haka, kamata ya yi su jira gwamnati ta san inda ta dosa sannan sai komai ya biyo baya."

Kara karanta wannan

Satar Akuya ta jawo matar aure ta buga wa mijinta gatari, ya mutu nan take

"Tsarin yin afuwa ba abu bane da kawai ake yi a rana ɗaya, sai an yi tsari sosai ta yadda za a samu sakamako mai kyau."
"Ina tunanin ba su da haƙuri ne. Mun sha tambayarsu menene takamaiman abin da suke so kuma me suke nema, amma babu wanda ya fito ya gaya mana."
"Idan aka kira su taro domin a tattauna babu wanda zai zo saboda suna cewa 'a fara yi mana afuwa', suna tsoron cewa idan suka zo za a cafke su."
"Saboda haka ta ina suke so mu tattauna da su? Kamar ba su san abin da suke so ba. Idan da za su fito su faɗi buƙatunsu, gwamnati za ta duba su, sannan idan abin da za ta iya yi ne, za mu yi."
"A yanzu dai ba mu san abin da suke so ba. Idan aka kira su taro ba za su zo ba."

- Mathew Abo

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya zama na farko a Arewa da ya amince zai fara biyan ma'aikata N70,000

Ƴan bindiga sun sace shugaban kwaleji

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikata uku da suka haɗa da mukaddashin shugaban kwalejin fasaha ta jihar Benue, da ke Ugbokolo, Dakta Emmanuel Barki.

Emmanuel Barki da sauran ma'aikata biyu na kwalejin da direbansu, an sace su ne a kan hanyar su ta dawowa zuwa Ugbokolo bayan sun je wani aiki a Makurdi, ranar Alhamis, 11 ga watan Yulin 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng