Dangote Ya Fara Shirin Sayar da Matatar Man Fetur Dinsa, An Samu Bayanai

Dangote Ya Fara Shirin Sayar da Matatar Man Fetur Dinsa, An Samu Bayanai

  • Alhaji Aliko Dangote ya fara shirin siyar da matatar man fetur ɗinsa wacce aka kwashe shekaru ana ginawa a jihar Legas
  • Attajirin wanda ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika ya ce a shirye yake ya siyar da matatar man fetur ɗin ga kamfanin NNPCL
  • Ya nuna cewa wasu mutane ba su ji daɗin yadda ya shigo cikin harkar man fetur ba shiyasa suke ƙoƙarin zame masa ƙarfen ƙafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aliko Dangote ya ce a shirye yake ya sayar da matatar man fetur ɗinsa.

Dangote ya ce ya shirya sayar da matatar man fetur ɗin ta biliyoyin daloli ga kamfanin NNPCL.

Kara karanta wannan

Dangote ya musanta zargin samar da dizal mara inganci, ya kalubalanci hukumar NMDPRA

Dangote zai siyar da matatarsa ga NNPCl
Dangote ya yi tayin siyar da matatarsa ga NNPPCL Hoto: Blomberg
Asali: Getty Images

Alhaji Aliko Dangote ya bayyana hakan ne dai yayin wata tattaunawa ta musamman da jaridar Premium Times a ranar Lahadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne bayan Dangote ya ƙalubalanci hukumar NMDPRA kan batun cewa man dizal da yake samarwa bai kai ingancin wanda ake shigo da shi daga ƙasar waje ba.

Meyasa Dangote zai siyar da matatarsa?

Attajirin ya yi magana ne a yayin da dangantaka ta fara yin tsami tsakaninsa da hukumomi a ɓangaren makamashi na Najeriya.

"Su (NNPCL) su zo su siya sannan su ci gaba da gudanar matatar man fetur ɗin yadda za su iya. Sun kira ni da mai yin kaka gida. Wannan zargin kuskure ne, amma ba komai. Aƙalla idan suka siya zan kauce na ba su waje."
"Tun daga shekarun 1970 muke fuskantar matsalae man fetur. Wannan matatar man fetur ɗin za ta taimaka wajen magance matsalar amma ga alamu wasu ba su jin daɗin cewa na shigo harkar."

Kara karanta wannan

Sanata Ali Ndume ya tura sako mai zafi ga Tinubu bayan cire shi daga mukaminsa

"Saboda haka a shirye nake na tafi, NNPPC su zo su siya, su ci gaba da gudanar da matatar man fetur ɗin."
"Kamar yadda kuka sani shekara ta 67 a duniya, a cikin ƙasa da shekara uku zan cika shekara 70. Abu kaɗan na ke buƙata na ƙarasa rayuwata. Ba zan iya tafiya da matatar ko wata kadara zuwa kabarina ba."
"Saboda haka a shirye nake na haƙura, su NNPC su zo su siya su ci gaba da gudanar da matatar. Aƙalla ƙasar nan ta samu kayayyaki masu inganci da samar da ayyukan yi.

- Alhaji Aliko Dangote

Dangote ya ci gyaran Tinubu da CBN

A wani labarin kuma, kun ji cewa Aliko Dangote ya ja hankalin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan ƙara kuɗin ruwa da babban bankin Najeriya (CBN) ya yi zuwa kaso 30%.

Aliko Dangote ya ce yin hakan zai ƙara durkusa sana'o'i tare da rufe ƙofa ga waɗanda suke ƙoƙarin fara sana'a a ƙasar nan

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng