“Ba Domin Cin Mutunci Ba Ne”: Gwamna Ya Fadi Dalilin Gyara a Dokar Masarautu
- Yayin da ake ta yada jita-jita kan sabuwar dokar masarautu, gwamnatin jihar Oyo ta yi karin haske kan abin da ake yadawa
- Gwamnatin ta ce dokar da Majalisar ta tabbatar wanda Gwamna Seyi Makinde ya sanyawa hannu ba ta da alaka da hana gadon kujerar
- Kwamishinan yada labarai a jihar, Dotun Oyelade ya bayyana damuwa kan yadda ake yada abin da kwata-kwata ba a fahimta ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - Gwamnatin jihar Oyo ta yi karin haske kan gyaran fuska game da masarautun jihar da ake ta zarge-zarge a kansu.
Gwamnatin jihar ta musanta zargin da ake yadawa cewa ta dauki matakin ne domin hana gadon kujerar Olubadan.
Masarautu: Gwamna ya fayyace sabuwar doka
An yi yada jita-jitar a lokacin bikin nadin sarautar sabon sarkin Ibadan da ake kira Olubadan, Oba Owolabi Olakulehin, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi bikin madin sarautar a ranar 12 ga watan Yulin 2024 inda aka raba litattafai dauke da sabuwar dokar yayin bikin, Premium Times ta tattaro.
Sabuwar dokar ta samu sahalewar Majalisar jihar Oyo wanda Gwamna Seyi Makinde ya sanyawa hannu.
Gwamnatin Oyo ta soki masu yada jita-jita
Kwamishinan yada labaran jihar, Dotun Oyelade ya ce akwai rashin adalci tsantsa kan abubuwan da mutane suke yadawa.
Oyelade ya ce rashin adalci ne a fara batun sabon sarki mai zuwa a gaba wanda a yanzu ne aka nada Olubadan bai yi ma ko mako daya ba.
Ya ce wasu tun yanzu har sun fara neman ganin karshen sabon Olubadan wanda ko mako daya bai yi ba.
An nada Olubadan na 43 a Oyo
Kun ji cewa bayan amincewar Gwamna Seyi Makinde a makonnin baya, a ranar Jumu'a 12 ga watan Yuli, 2024 za a nada sabon Olubadan.
Sabon sarkin, Oba Owolabi Akinloye Olakulehin ya kafa tarihin zama Olubadan na 43 wanda ya ke da shekara 85 ya zama sabon sarkin ƙasar Ibadan.
Bayanai sun nuna cewa jim kaɗan bayan kammala naɗa masa rawanin sarautar, Oba Olakuleyin ya koma fadar Ile Osemeji da ke unguwar Oja Oba a birnin Ibadan.
Asali: Legit.ng