Duk da Rasa Mukaminsa Sanata Ndume Ya Ci Gaba da Caccakar Shugaba Tinubu

Duk da Rasa Mukaminsa Sanata Ndume Ya Ci Gaba da Caccakar Shugaba Tinubu

  • Sanata Ali Ndume, wanda aka tsige daga kan muƙamin babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa, ya ci gaba da caccakar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
  • Kalaman da Sanata Ali Ndume ya yi a baya kan Shugaba Tinubu ne ya sa aka tsige shi a matsayin babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa
  • Ndume ya ce sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da gwamnatin tarayya da ƴan ƙwadago suka amince da shi, ya yi kaɗan idan aka kwatanta da irin wahalar da ƴan Najeriya ke ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya ci gaba da sukar Shugaba Bola Tinubu duk da tsige shi daga muƙaminsa na babban mai tsawatarwa a majalisar dattawan Najeriya.

Kara karanta wannan

Sanata Ali Ndume ya tura sako mai zafi ga Tinubu bayan cire shi daga mukaminsa

Kalaman Ndume kan gwamnatin Shugaba Tinubu suka jawo aka tsige shi daga muƙaminsa sannan jam’iyyarsa ta nemi ya fice ya koma jam’iyyar adawa.

Ndume ya caccaki Shugaba Bola Tinubu
Sanata Ali Ndume ya ce albashin N70,000 ya yi kadan Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Sen Mohammed Ali Ndume
Asali: Twitter

Ndume ya faɗawa Tinubu gaskiya kan albashi

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Sanata Ndume ya ce zai ci gaba da faɗin gaskiya ga masu mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin wata tattaunawa da manema labarai Ndume yayi tsokaci akan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da Tinubu da NLC suka amince da shi.

Ya bayyana cewa, duk da cewa ƙarin wani mataki ne mai kyau, amma ya yi kaɗan wajen magance wahalhalun da ƴan Najeriya ke ciki, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

Sanata Ndume ya kwatanta sabon mafi ƙarancin albashin da farashin buhun shinkafa, inda ya jaddada cewa akwai buƙatar a ƙara ƙaimi domin rage raɗaɗin talaucin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya maida martani ga Ganduje, ya faɗi yadda Buhari da Tinubu suka jawo shi APC

"Mutane suna shan wahala, mutane sun fusata, mutane ba su cikin farin ciki. Na yi murna cewa shugaban ƙasa da NLC sun ƙara albashi zuwa N70,000 wanda hakan abu ne mai kyau."
"Amma ana buƙatar abin da ya fi haka saboda magana ta gaskiya wannan kuɗin buhun shinkafa ne, kuɗin da za su sayi buhun shinkafa ne ko suka yi daidai da kuɗin shinkafa."
"Saboda haka ina kira ga shugaban ƙasa da ya buɗe kunnuwansa ya saurari koken da mutane suke yi."

- Sanata Ali Ndume

Ndume ya magantu kan rasa muƙaminsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Ali Ndume, ya ce ko kaɗan bai yi laifi ba kan sukar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Ndume ya kuma ce babu wani dalili da zai sanya ya ba da haƙuri duk da tsige shi da aka yi daga kan muƙamin babban mai tsawatarwa na majalisar dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng