'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 2, Sun Sace Wasu Matafiya 5 a Wani Hari

'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 2, Sun Sace Wasu Matafiya 5 a Wani Hari

  • Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai farmakin ta'addanci kan matafiyan da ba su ji ba, ba su gani ba a jihar Ondo
  • Ƴan bindigan waɗanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun hallaka mutum biyu ciki har da direban motar tare da sace matafiya mutum biyar
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce ta tura jami'anta domin cafko ƴan bindigan tare da kuɓutar da mutanen da suka sace

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Wasu ƴan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe matafiya biyu tare da yin garkuwa da wasu mutum biyar a jihar Ondo.

Ƴan bindigan sun tare matafiyan ne a babbar hanyar Ifon zuwa Owo a jihar Ondo.

Kara karanta wannan

Satar Akuya ta jawo matar aure ta buga wa mijinta gatari, ya mutu nan take

'Yan bindiga sun kai hari a Ondo
'Yan bindiga sun hallaka mutum biyu a Ondo Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yadda lamarin ya auku

Jaridar The Punch ta ce ƴan bindigan sun harbe direban motan tare da wata mata fasinja a wurin da lamarin ya faru a yammacin ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindigan sun tafi da wasu fasinjoji biyar ciki har da wani ɗan bautar ƙasa. Sai dai mutum biyu daga cikinsu sun yi nasarar tserewa, inda suka samu raunuka daban-daban, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Ɗaya daga cikin mazauna yankin ya bayyana cewa motar ta fito ne daga jihar Anambra inda ta nufi Owo da Akure a jihar Ondo a lokacin da ƴan bindigan suka farmaketa.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ƴan sandan jihar Ondo, Fumilayo Odunlami-Omisanyan, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho.

Ta bayyana cewa an tura tawagar ƴan sanda yankin, kuma a halin yanzu sun shiga dajin da ke kusa da wajen domin kamo masu garkuwa da mutanen da kuma kuɓutar da mutanen da suka sace.

Kara karanta wannan

Bayan rage albashi 'yan majalisa sun nemi muhimmiyar bukata wajen 'yan Najeriya

Ƴan bindiga sun kai hari a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun hallaka mutum huɗu tare da yin garkuwa da wasu mutum 150, ciki har da jarirai ƴan watanni shida da takwas.

Wannan ya faru ne a farmakin da miyagun suka kai kauyen Dan Isa dake ƙaramar hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara a ranar Lahadi, 14 ga watan Yulin 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng