Duk da Dokar Hana Fita, ’Yan Bindiga Sun Kutsa Kauye da Dare, Sun Hallaka Jama’a
- 'Yan bindiga sun bijirewa dokar hana fita a jihar Benue inda suka kutsa cikin kauye tare da hallaka mutane 18 yayin harin
- Maharan sun kutsa kauyen Mbacher da ke karamar hukumar Katsina-Ala da misalon karfe 11.00 na daren jiya Juma'a
- Shugaban karamar hukumar, Justine Shaku shi ya tabbatar da harin inda ya ce sojoji sun kawo dauki amma sun yi latti
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Benue - Wasu 'yan bindiga sun shammaci mazauna wani kauye da tsakar dare inda suka hallaka mutane 18 a jihar Benue.
Lamarin ya faru ne da karfe 11.00 na daren jiya Juma'a 19 ga watan Yulin 2024 a kauyen Mbacher da ke karamar hukumar Katsina-Ala.
Benue: 'Yan bindiga sun tafka barna
Harin na zuwa ne bayan gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita daga shida na yamma zuwa safiya, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Maharan sun yi fatali da dokar inda suka fito tare da hallaka mazauna yankunan da dama tare da tafka barna.
Maharan sun jera mutanen kamar za su yi musu jawabi amma daga bisani sai suka bude musu wuta, Tribune ta tattaro.
Benue: Shugaban karamar hukuma ya magantu
Shugaban karamar hukumar Katsina-Ala, Justine Shaku ya yi Allah wadai da harin inda ya ce maharan sun gama barna kafin zuwan sojoji.
"Da misalin karfe 11.00 na daren jiya Juma'a mun samu labarin cewa mahara sun shigo kauyen inda suke shiga gida-gida suna fito da su."
"Na yi gaggawar samun dakarun sojoji a Tor Doonga sai dai abin takaici kafin isowarsu maharan har sun hallaka mutane sun tsere."
- Justine Shaku
Shaku ya kara da cewa wasu daga cikin mutane sun gamu da raunuka yayin harin inda ya jajantawa wadanda suka rasa rayukansu.
'Yan bindiga sun sace shugaban Kwaleji
Kun ji cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da mukaddashin shugaban kwalejin fasaha ta jihar Benue, da ke Ugbokolo, Dakta Emmanuel Barki.
Barki da sauran ma'aikata biyu na kwalejin da direbansu, an sace su ne a kan hanyar su ta dawowa zuwa Ugbokolo bayan sun je wani aiki a Makurdi.
Asali: Legit.ng