Matasan Arewa Sun Soki Ministan Buhari Kan Goyon Bayan Zanga Zanga
- Kungiyar Arewa Progressives for Good Governance ta caccaki tsohon Ministan matasa, Solomong Dalung kan zanga-zanga
- Kungiyar ta ce duk wani dan Arewacin Najeriya da ke kiran zanga-zanga ba shi da adalci saboda bai yi a mulkin Muhammadu Buhari ba
- Shugaban kungiyar, Ibrahim Musa Bichi shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa inda ya ce komai zai daidaita ba da jimawa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kungiyar matasan Arewa ta caccaki tsohon Minista, Solomon Dalung kan goyon bayan zanga-zanga a kasar.
Kungiyar mai suna Arewa Progressives for Good Governance (APGG) ta barranta da tsohon Ministan matasa a mulkin Muhammadu Buhari.
Zanga-zanga: Matasan Arewa sun caccaki Dalung
Shugaban kungiyar, Ibrahim Musa Bichi shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Vanguard ta samu inda ya ce tabbas ana shan wahala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bichi ya ce duka wahalar da ake fuskanta akwai lokacin da za su wuce wanda ake sa ran komai zai daidaita yadda ya kamata.
Ya ce ba gaskiya ba ne cewa manyan mutane a Najeriya da suka hada tsofaffin sanataci da masu ci za su shiga zanga-zangar da za a yi.
"Mun fahimci irin halin kunci da ake ciki a Najeriya, amma muna da ba da tabbacin komai zai wuce kuma akwai haske a gaba."
"Duk wani dan Arewa da ke kiran yin zanga-zanga game da gwamnatin Bola Tinubu ba shi da adalci ko kadan."
"Dan yankinmu Muhammadu Buhari ya yi mulki har shekaru takwas amma babu wanda ya fito zanga-zanga a lokacin."
- Ibrahim Musa Bichi
Wannan na zuwa ne bayan zargin Dalung ya nuna goyon bayansa game da zanga-zangar da ake shirin yi game da halin kunci da ake ciki.
Tsohon Ministan ya wallafa cewa bai kamata a take hakkin 'yan kasa wurin gudanar da zanga-zanga ba a kasar.
Murtala Asada ya magantu kan zanga-zanga
Kun ji cewa fitaccen malamin addini Musulunci, Malam Murtala Bello Asada ya karfafi matasa kan fita zanga-zanga a kasar.
Murtala Asada ya ce masifar da al'umma ke ciki musamman a Zamfara da Sokoto ya fi abin da ake zaton zanga-zanga za ta jawo.
Asali: Legit.ng