'Yancin Kananan Hukumomi: Gwamnan Arewa Ya Fadi Matsayarsa

'Yancin Kananan Hukumomi: Gwamnan Arewa Ya Fadi Matsayarsa

  • Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya yi magana kan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi
  • Gwamna Radda ya bayyana cewa tuni a jihar Katsina ƙananan hukumomi suna samun wani kaso na cin gashin kai
  • Hakan na zuwa ne dai bayan Kotun Ƙoli ta ba ƙananan hukumomi da ke faɗin ƙasar nan ƴancin cin gashin kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya ce zai aiwatar da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan cin gashin kan ƙananan hukumomi.

Kotun Ƙolin dai ta ba ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kansu biyo bayan ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar a kan gwamnoni.

Kara karanta wannan

Gagarumar zanga zanga ta barke a jihar Arewa, bayanai sun fito

Gwamna Radda ya yi magana kan 'yancin kananan hukumomi
Gwamna Dikko Radda zai mutunta hukuncin Kotun Koli Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Bayan haka, majalisar dattawa ta gabatar da ƙudirin kafa hukumar da za a ɗorawa alhakin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Radda ya ce kan ƴancin ƙananan hukumomi?

Daily Trust ta ce Gwamna Radda a wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar ranar Asabar a Abuja, ya ce ƙananan hukumomin jihar Katsina sun daɗe suna samun wani kaso na cin gashin kai.

Sanarwar ta ambato Gwamna Radda yana magana a yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Katsina.

"Ban kira ku nan ba domin fassara hukuncin. Jihar Katsina jiha ce mai bin doka da oda kuma za ta yi aiki a ƙarƙashin tsarin mulkin tarayyar Najeriya."
"Na buƙaci antoni janar na jiha ya ba ni cikakken rahoto kan hukuncin Kotun Ƙolin ta fuskar doka."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta ba gwamnan PDP shawara kan 'yancin kananan hukumomi

"Kamar yadda kuka sani na taɓa zama shugaban ƙaramar hukumar Charanchi a zamanin gwamnatin shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’adua."
"Na san yadda ake gudanar da harkokin yau da kullum na mulki a ƙaramar hukumata, kuma ina da cikakkiyar masaniya kan ƙalubale da raɗaɗin da yawancin ku ke fuskanta."

- Dikko Umaru Radda

Gwamna Radda ya samu yabo

Legit Hausa ta tuntuɓi wani mazaunin jihar Katsina mai suna Muhammad Auwal wanda ya yabawa gwamnan bisa matakin da ya ɗauka na mutunta hukuncin kotun.

Ya bayyana cewa tabbas ba ƙananan hukumomin ƴancin cin gashin kansu zai kawo ci gaba sosai ga mutanen da ke karkara domin gwamnati za ta ƙara matsowa kusa da su.

"Eh tabbas a Katsina ana yin zaɓen ƙananan hukumomi kuma suna gudanar da wasu ayyukan saboda ana sakar musu mara. Amma yanzu da za su samu cikakken ƴancin cin gashin kansu muna sa ran abubuwa za su inganta sosai."

Kara karanta wannan

"Dalilin da ya sa 'yancin cin gashin kan kananan hukumomi ba zai yi aiki ba" Inji Tsohon gwama

- Muhammad Auwal

Gwamna Radda ya tafi hutu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda ya miƙawa mataimakinsa, Faruk Lawal Jobe ragamar mulkin jihar.

Gwamna Radda ya miƙa masa mulkin ne domin tafiya hutun wata ɗaya wanda zai fara daga ranar Alhamis, 18 ga watan Yulin 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng