Zanga Zangar Adawa da Tinubu: Gwamnan Arewa Ya Fadi Abin da Matasan Jiharsa Za Su Yi

Zanga Zangar Adawa da Tinubu: Gwamnan Arewa Ya Fadi Abin da Matasan Jiharsa Za Su Yi

  • Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya ce matasan jihar masu son zaman lafiya ba za su shiga cikin zanga-zangar da ake shirin gudanarwa ba
  • Gwamnan ya buƙaci masu son yin zanga-zangar da su haƙura su zo a tattauna domin samun mafita halin da ake ciki a ƙasa
  • Ya kuma sanar da fitar da tan 50,000 na hatsi wanda za a sayar da shi a kan kaso 50% na farashin da ake sayarwa a kasuwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya yi magana kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar nan.

Gwamna Bago ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa matasan jihar Neja ba za su shiga zanga-zangar ba wacce za a yi a faɗin ƙasar nan daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya fallasa sunayen masu shirya zanga zangar adawa da gwamnati

Gwamna Bago ya ce matasan Neja ba za su yi zanga-zanga ba
Gwamna Bago ya ce matasan Neja ba su shiga zanga-zanga ba kan halin kunci Hoto: Mohammed Umaru Bago
Asali: Facebook

Gwamna Bago ya bayyana haka ne a wani taro da aka yi a birnin Minna, babban birnin jihar Neja, cewar rahoton jaridar The Guardian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Gwamna Bago ya ce kan zanga-zanga?

Gwamnan ya sha alwashin cewa matasan jihar suna son zaman lafiya kuma ba za su shiga cikin shirin yin zanga-zangar ba kan halin ƙuncin da ake ciki a Najeriya, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"Mu a matsayinmu na matasan jihar Neja mun nesanta kanmu daga zanga-zangar da ake shirin yi a fadin ƙasar nan saboda bamu son fitina kuma muna son zaman lafiya da kwanciyar hankali."
"Kuna iya fara zanga-zanga amma ba za ku iya kawo ƙarshen zanga-zanga ba. Ga matasan da ke son yin wannan zanga-zangar, ku ɗauki dangana. Mu koma kan tattaunawa domin samar da hanyar da ta dace."

- Mohammed Umaru Bago

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fadi dalilin rokon mazauna Yobe su kauracewa zanga zanga

Bago ya rage farashin hatsi a Neja

Gwamnan ya kuma amince da fitar tan 50,000 na hatsi wanda a cewarsa za a sayar da shi a kan kaso 50% na farashin da ake sayar da shi a halin yanzu.

Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su tashi tsaye wajen sanya ido tare da tabbatar da cewa an sayar da hatsin bisa tsari.

A bar matasa su yi zanga-zanga

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wata mazauniyar garin Suleja a jihar Neja mao suna Joy Egbunu wacce ta bayyana cewa ya kamata a bar matasa su fito su nuna fushinsu kan halin da ake ciki a ƙasa.

Joy wacce ta nuna cewa Gwamna Bago na ƙoƙari a jihar wajen ganin ya rage raɗaɗin da mutane suke ciki.

"Ya kamata matasa su fito su nuna fushinsu domin tallafin da ake cewa ana bayarwa ba kowa ba ne yake samu."

Kara karanta wannan

Dan gwamnan Borno ya kashe ɗan China a gidan rawa? Umar Zulum ya yi bayani a bidiyo

- Joy Egbunu

Tinubu zai shilla ƙasar waje

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu zai tashi daga Najeriya zuwa ƙasar Ghana a ranar Asabar, 20 ga watan Yulin 2024.

Shugaban ƙasan zai ziyarci ƙasar ne domin halartar taron tsakiyar shekara na ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) wanda za a gudanar a ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng