Satar Akuya Ta Jawo Matar Aure Ta Buga Wa Mijinta Gatari, Ya Mutu Nan Take

Satar Akuya Ta Jawo Matar Aure Ta Buga Wa Mijinta Gatari, Ya Mutu Nan Take

  • Wata matar aure ƴar kimanin sheksra 40 Lydia Aji ta hallaka mijinta da gatari yayin da saɓani ya shiga tsakaninsu a jihar Borno
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta ce tuni jami'ai suka kama matar bayan samun rahoton abin da ya faru a ƙaramar hukumar Chibok
  • Mai magana da yawun ƴan sandan, Nahum Kenneth ya ce ma'auratan sun kaure da faɗa ne kan satar da ɗiyarsu ƴar shekara 13 ta yi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Ƴan sanda sun kama wata mata mai suna Lydia Aji, ƴar kimanin shekaru 40 a duniya bisa zargin kashe mijinta da gatari a jihar Borno.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, Nahum Kenneth ne ya bayyana haka a madadin kwamishinan ƴan sandan Borno, CP Yusuf Lawal.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya zama na farko a Arewa da ya amince zai fara biyan ma'aikata N70,000

Taswirar jihar Borno.
An kama.wata matar aure da ta kashe mijinta da gatari a Borno
Asali: Original

Ya ce matar da ake zargin ta yi ja-in-ja da marigayin a kan batun satar akuya da ‘yarsu mai shekaru 13, Rachael ta yi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Borno: Yadda matar ta halaka mijinta

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa bayanai sun nuna magidanci ya mutu nan take bayan matar ta kwaɗa masa gatari a lokacin da suke cacar baki.

Nahum Kenneth ya ce:

"Wani mutumi Bulama Mulikabu daga kauyen Kautikari a ƙaramar hukumar Chibok ya kai rahoton abin da ya faru caji ofis na garin Chibok ranar 4 ga watan Yuli.
"Ya shaidawa ƴan sanda cewa a wannan rana Lydia Aji da mijinta Aji Makama sun sami saɓani har ta kai faɗa ya kaure a tsakaninsu, matar ta ɗauki gatari ta buga wa mijin nan take ya mutu.

Abin da ya haɗa ma'auratan faɗa

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi wa ƴan ƙwadago alƙawari 1 bayan amincewa da albashin N70,000 a Aso Villa

Mai magana da yawun ƴan sandan ya ƙara da cewa a lokacin da faɗa ya kaure tsakanin ma'auratan, magidancin ya umarci matarsa da ƴarsa da ta yi sata su bar masa gida.

Daily Post ta tattaro kakakin ƴan sandan na cewa:

"Da muka zurfafa bincike mun gano cewa ma'auratan sun samu saɓanin da ya kai ga faɗa ne kan diyarsu, Rachael Aji yar shekara 13 wacce ta sato akuya ta siyar.
"Sakamakon haka ne magidancin ya ɗauki zafi har ya umarci matarsa ta ƴarsa su bar masa gida. Har yanzu dai muna bincike a kan lamarin."

Borno: Wata Farfesa ta mutu a gareji

A wani rahoton kuma rundunar 'yan sanda a jihar Borno ta tabbatar da mutuwar wata Farfesar Jami'ar Maiduguri a wani irin yanayi.

Marigayiyar mai suna Farfesa Ruth Wazis wacce tsohuwar shugabar tsangayar harkokin kasuwanci ce ta rasu a cikin garejin mota a gidanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262