Kalamai a Kan Gwamnatin da Suka Tsumbula Sanata Ndume Cikin Ruwan Zafi a APC da Majalisa

Kalamai a Kan Gwamnatin da Suka Tsumbula Sanata Ndume Cikin Ruwan Zafi a APC da Majalisa

  • Muhammad Ali Ndume ya gamu da fushin abokan aikinsa a majalisa saboda wasu kalamai da ya yi a fili kwanaki
  • Sanatan na Kudancin jihar Borno ya ba da labarin yadda ya tunkari gwamnati kan halin kuncin da talakawa su ke ciki
  • Ko da Ali Ndume ya nunawa masu mulki rayuwa ta yi wahala, sai aka fada masa cewa sharrin ‘yan adawa ne kurum

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - A watan Yunin 2023, Muhammad Ali Ndume ya goyi bayan Godswill Akpabio ya zama shugaban majalisar dattawa na kasa.

A karshe Muhammad Ali Ndume ya samu matsayi da kujera a kwamiti mai tsoka, shekara guda bayan nan sai labarin ya canza.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya maida martani ga Ganduje, ya faɗi yadda Buhari da Tinubu suka jawo shi APC

Ndume
Sanata Muhammad Ali Ndume ya soki gwamnatin Bola Tinubu a Najeriya Hoto: Imranmuhdz
Asali: Twitter

Jawabin da ya jefa Ali Ndume a matsala

Legit ta yi waiwaye, ta dauko kalaman da suka jefa Ali Ndume a tashar Arise a cikin matsala, ta kai ya rasa matsayi a majalisar dattawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan za a tuna, a hirar da aka yi da shi a kwanakin bayan, Sanata Ndume ya yi bayanin halin da talaka yake ciki a mulkin Bola Tinubu.

“Na aika masu sako cewa kun san mutane sun fusata? Ku na yin wani abin a kai?” Amsar ita ce, 'eh mu na sane. Aikin ‘yan adawa ne.'"
"A nan na ce mun bani mun lalace. Domin babu ‘yan adawan da za su kona gidan da su ke ciki."

- Sanata Ali Ndume

Sanata Ndume ya ce akwai matsala

Ndume ya cigaba da cewa muddin kasar nan ta tabarbare, lamarin ba zai shafi gwamnati kadai ba, zai taba har jam’iyyar hamayya.

Kara karanta wannan

Zargin biyan malamai N16m domin rufe masu baki ya fusata Sheikh Mansur Sokoto

A cewarsa idan masu mulki su ka fara daura laifi a kan ‘yan adawa, shi karon kan shi da kuma shugaban kasar su na cikin matsala.

Tsadar abinci ya tada hankalin Ndume

A hirar da aka yi da shi, jagoran na APC ya koka da yadda farashin kayan abinci su ka yi mummunan tashi, abinci ya gagara.

"Buhun shinkafa, masara sun kai kusan N100, 000."
"Matata ta fada mani kwandon tumaturi ma ya kai kusan N100, 000, haka zalika albasa."

- Sanata Ali Ndume

'An hana mutane ganin Tinubu' - Ndume

Gidan talabijin ya rahoto ‘dan siyasar ya na zargin barayi su ka zagaye shugaban kasa Bola Tinubu duk da kyakkyawar niyyarsa.

Idan zancensa gaskiya ne, an katange Bola Tinubu kuma an hana mutane su zauna da shi.

Ndume ya ce Naira ta rasa kima sannan kaya suna kara tsada, ana Shirin zanga-zanga amma masu mulki ba su hankalta ba.

Kara karanta wannan

Sukar Tinubu: Sanata Ndume ya mayar da martani kan sauke shi a muƙamin Majalisa

Shi dai ‘dan majalisar yana fatan ya ari bakin talakawan da suka zabe shi, ya ci masu albasa domin al’umma su na wayyo Allah.

Ndume ya rasa rikon babban kwamiti

Bayan sauke shi daga matsayin shugaban masu tsawatarwa, an tsige Sanatan daga mataimakin shugaban kwamitin kasafi.

Ana da labari cewa sanatan na APC mai mulki ya ki karbar wannan mukami, ya ce babu abin da ya hada shi da harkokin yawon bude ido.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng