Gwamnan PDP Ya Yiwa Ma'aikata Albishir Kan Batun Biyan N70,000
- Gwamnan jihar Osun ya yi alkawarin biyan ma'aikatan jihar sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 da gwamnatin tarayya da ƴan ƙwadago suka amince da shi
- Gwamna Ademola Adeleke ta hannun kwamishinan yaɗa labaransa ya bayyana cewa walwalar ma'aikata na daga cikin abin da yake ba da fifiko a kai
- Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnan ba zai kasance cikin waɗanda ba zaɓsu biya ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashin na N70,000
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Osun - Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ya yi magana kan batun biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 duk wata.
Gwamna Ademola Adeleke a ranar Juma'a, 19 ga watan Julin 2024 ya yi alƙawarin cewa zai biya ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashin na N70,000.
Gwamna Adeleke zai biya albashin N70,000
Jaridar The Nation ta ce Gwamna Adeleke ya bayyana mata hakan ne ta hannun kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Kolapo Alimi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnan yana mayar da hankali sosai wajen ganin cewa ma'aikata sun kasance cikin walwala.
"Gwamnanmu mai ƙaunar ma'aikata ne, ajandarsa ta farko ita ce fifita jin daɗin ma'aikata waɗanda ke aiki tuƙuru da waɗanda ba su yi."
"Gwamna Ademola Adeleke ba zai kasance cikin waɗanda ba za su biya sabon mafi ƙarancin albashi ba."
"Jihar Osun ba za ta taɓa bijirewa doka ba kan mafi ƙarancin albashi. Gwamna Adeleke zai yi amfani da ita."
- Kolapo Alimi
Karanta wasu labaran kan mafi ƙarancin albashi
- Magana ta kare: Tinubu ya fadi sabon mafi karancin albashi tare da ɗaukar alkawura 3
- Mafi karancin albashi: 'Yan kwadago sun fadi dalilin amincewa da N70,000
- N70,000: Kalubale 5 da ke gaban 'yan kwadago da ma'aikata bayan karin albashi
Gwamna Alia zai biya ma'aikata N70,000
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Benue Hyacinth Alia, ya ce gwamnatinsa a shirye take ta biya ma'aikatan jihar N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.
Gwamnan na jam'iyyar APC ya jaddada cewa gwamnatinsa ta riga ta yi maganin ɓarayi, ta tsohe duka wata hanyar da kuɗin bautul-mali ke sulalewa.
Asali: Legit.ng