Gwamnan APC Ya Zama Na Farko a Arewa da Amince Zai Fara Biyan Ma'aikata N70,000

Gwamnan APC Ya Zama Na Farko a Arewa da Amince Zai Fara Biyan Ma'aikata N70,000

  • Rabaran Hyacinth Alia ya bayyana cewa ya shirya tsaf domin fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 a jihar Benuwai
  • Gwamna Alia ya bayyana haka ne awanni 24 bayan Bola Tinubu da ƴan kwadago sun cimma matsaya a taron da suka yi ranar Alhamis
  • Ya ce gwamnatin jihar Benuwai ta samu ƙarin kudaden shiga kuma ta tsohe duk wata hanya da ake satar dukiyar talakawa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Gwamnan Benue Hyacinth Alia, ya ce gwamnatinsa a shirye take ta biya ma'aikatan jihar N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Gwamna Alia ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai a Makurɗi, babban birnin jihar Benuwai ranar Jumu'a, 19 ga watan Yuli, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya yiwa ma'aikata albishir kan batun biyan N70,000

Gwamna Alia na jihar Benue.
Gwamna Alia ya shirya fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi a Benuwai Hoto: Rev Fr Hyacinth Alia
Asali: Facebook

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ta riga ta yi maganin ɓarayi, ta tsohe duka wata hanyar da kuɗin bautul-mali ke sulalewa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Alia ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali sosai domin ganin komai ya koma kan turbar da ta dace a jihar da ke Arewa ta Tsakiya.

Kuɗin shiga sun ƙaru a Benue

A rahoton Tribune Nigeria, gwamnan ya ce:

"Abubuwa sun taɓarɓare sakamakon matsin tattalin arziki amma matakan da muka ɗauka sun fara haifar da ɗa mai ido, al'amura sun fara dawowa daidai.
"Hatta kuɗaɗen shigar mu sun karu, yanzu ya rage namu mu toshe hanyoyin da ɓarayi ke samun damar sata domin mu ga nawa za mu iya tarawa."

Gwamna Alia ya shirya biyan N70,000

Dangane da batun sabon mafi ƙarancin albashi da Bola Tinubu ya sanar ranar Alhamis, Gwamna Alia ya ce gwamnatinsa za ta iya biyan N70,000.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamna ya 'sauya sheka' zuwa APC, ya faɗi abin da ya riƙe shi a PDP

"Za mu iya biyan (mafi ƙarancin albashi) idan mu ka maida hankali, duk abin da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi, mu mabiya ‘yan kasa ya kamata mu bi sahu.
"Idan ba ma'aikata babu gwamnati saboda haka ya kamata mu biya ma'aikata da adadin da gwamnatin tarayya da ƴan kwadago suka amince da shi."

- Gwamna Hyacinth Alia.

Sarkin Gaya ya karɓi takardar naɗi

A wani rahoton kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bai wa Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Abdulkadir takardar kama aiki a gidan gwamnatin jihar Kano.

Sarkin yana ɗaya daga cikin sarakuna biyar da gwamnan ya tube amma ya koma kan mulkin bayan kirkiro masarautu masu daraja ta biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262