Gwamnati ta Fadi Dalilin Rokon Mazauna Yobe su Kauracewa Zanga Zanga
- Gwamnatin Yobe ta nemi jama'ar jihar su kauce wa shiga zanga-zangar gama gari da ake shirin gudanar wa a ranar 1 Agusta, 2024 kan matsin rayuwa
- Kwamishinan harkokin cikin gida, yada labarai da al'adu, Abdullahi Bego ne ya yi rokon ta cikin sakonnin da ya fitar don nuna rashin goyon bayan zanga-zanga
- Abdullahi Bego na ganin bai kamata mazauna Yobe su shiga zanga-zanga da zai iya jawo rashin tsaro a ihar ba ana tsaka da farfado wa daga Boko Hram
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Yobe - Gwamnatin Mai Mala Buni ta roki al'umar jihar Yobe da su guji shiga zanga-zangar gama gari da wasu ke kokarin hada wa a kasar nan saboda matsin tattalin arziki.
Gwamnatin na ganin an samu gagarumar nasarar tun bayan bullar iftila'in Boko Haram da ya hana al'ummar jihar da kewaye sakat, kuma bai kamata a jawo wani rashin kwanciyar hankalin ba.
A wasu jerin sakonni biyu da kwamishinan harkokin cikin gida, yada labarai da al'adu na jihar Yobe, Abdullahi Bego ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce bai kamata jama'a su yi zanga-zanga ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Yanzu mu ke farfado wa," Gwamnatin Yobe
Gwamnatin jihar Yobe ta shawarci mazauna garin su guji zanga-zanga da zai iya dagula lamarin tsaron yankin.
A wata sanarwa daban da Babban nataimaki na musamman ga gwamna Buni a kan sadarwar kafafen zamani, Yusuf Ali ya fitar, ya ce shiga zanga-zanga zai rikita zaman lafiya.
Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni na ganin yanzu yankin ke farfaɗo wa daga tashe-tashen hankula da 'yan kungiyar Boko Haram su ka kakaba wa jihar, Daily Post ta wallafa.
Zanga-zanga: Ohanaeze ta shawarci kabilar Ibo
A baya mun ruwaito cewa kungiyar 'yan kabilar Ibo ta Ohanaeze ta shawarci 'yan kabilar da ke zaune a Arewa su guji shiga zanga-zangar da ake shirin yi a watan Agusta.
Kungiyar ta kuma shawarci 'yan kabilar Ibo da ke zaune a Kudu maso Yamma da ka da su shiga zanga-zangar saboda fargabar yadda aka saba samun matsala a irin wadannan taruka a baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng