Kano: Bayan Naɗa Sarakuna 3, Gwamna Abba Kabir Ya Baiwa Sarkin Gaya Takarda

Kano: Bayan Naɗa Sarakuna 3, Gwamna Abba Kabir Ya Baiwa Sarkin Gaya Takarda

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bai wa Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Abdulkadir takardar kama aiki a gidan gwamnatin jihar Kano
  • Sarkin yana ɗaya daga cikin sarakuna biyar da gwamnan ya tube amma ya koma kan mulkin bayan kirkiro masarautu masu daraja ta biyu
  • Gwamnatin Kano ta bakin Sanusi Dawakin Tofa ta ce an mayar da basaraken kan karagar mulki ne bisa la'akari da cancantarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Abdulkadir ya karɓi takardar naɗinsa a hukumance daga hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano.

Aliyu Abdulƙadir ya koma kan karagar mulki bayan Gwamna Abba Kabir ya naɗa shi tare da wasu mutum biyu a matsayin sarakuna masu daraja ta biyu.

Kara karanta wannan

Kano: Sarki Sanusi II ya koka kan halin kunci da ake ciki, ya yabawa gwamnatin Abba

Gwamna Abba da Sarkin Gaya.
Sarkin Gaya da aka mayar ya karɓi takardar kama aiki daga Gwamna Abba a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

A ranar Laraba, gwamnan ya sanar da naɗin sarakuna uku da za su jagoranci sababbin masarautun da ya kirkiro a jihar Kano, kamar yadda The Cable ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin Abba na dawo da Sarkin Gaya

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce an mayar da Sarkin Gaya kan mulki saboda ya cancanta.

"Idan za ku iya tunawa Sarkin Gaya ne kadai ya rungumi kaddara a matsayin haka Allah ya tsara a lokacin da aka rushe masarautu biyar kuma aka sauke duka sarakuna.
"Dukkan masu rike da sarauta da masu naɗin sarki a masarautar gaya sun rako basaraken zuwa gidan gwamnatin Kano," in ji Sanusi.

Yadda aka dawo da Sarki Sanui II

Idan ba ku manta da Gwamna Abba ya rushe masarautu biyar da ya taras a Kano tare da tuɓe dukkan sarakunan da Ganduje ya naɗa a lokacin mulkinsa.

Kara karanta wannan

Kofar Mata: Abba Kabir, Kwankwaso sun tura sako ga kwamishina bayan iftila'in gobara

Bayan haka kuma gwamnan ya sanar da dawo da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16, Premium Times ta rahoto.

A lokacin da aka tsige shi daga karagar Sarkin Gaya, Aliyu Abdulƙadir ya ce ya amince da abin da Allah ya kaddaro masa kuma ba zai kalubalanci gwamnatin Abba ba.

Sarkin Gaya ya karɓi takardar naɗi

A ranar Talata da ta gabata, gwamnan Kano ya rattaba hannu kan dokar kafa masarautu uku masu daraja ta biyu a jihar.

Bayan sanar da sunayen sarakuna masu daraja ta biyu ranar Laraba, Gwamna Abba ya ba Sarkin Gaya da ya dawo da shi kan mulki takardar naɗi yau Jumu'a.

Sarki Sanusi II ya koka kan tsadar rayuwa

Kuna da labarin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan raba takin zamani ga al'ummar jihar baki daya.

Sanusi II ya nuna damuwa kan halin kunci da ake ciki a yanzu musamman tsadar kayan masarufi inda har ta kai ya shawarci masu hali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262