Kwanaki 5 a Jere Darajar Naira Na Cigaba da Ruguzowa a Kasuwar Canji
- An canjar da Naira a kan N1,600 kowacce Dala a kasuwar hada-hadar kudaden kasashen waje a ranar Alhamis, wanda ke nuna samun karuwar faduwar darajarta
- Kwanaki biyar ke nan ana samun faduwar kimar darajar Naira a kasuwar musayar kudi ta kasa inda aka samu ribar N20 a kan yadda aka sayar a ranar Laraba
- Farashi mafi sauki da aka canjar da Dala a ranar Alhamis 18 Yuli, 2024 ya kai N1,500 a kasuwar musayar kudin gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Darajar Naira na ci gaba da faduwa a kasuwar gwamnati yayin da ta jera kwanaki biyar ta na faduwa ba kakkauta wa.
An canzar da Naira a kan N1,620 kowacce Dala a ranar Alhamis 18 Yuli, 2024 a farashinta mafi tsada da aka yi hada-hada a lokacin.
Bayanai daga kamfanin kula da hada-hadar canji ta kasa, FMDQ Exchange ya nuna cewa kimar kudin Najeriya ya ragu da 0.3% a kan yadda aka yi canjinsa a ranar 17 Yuni, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan kasuwar canji sun samu ribar 20%
Jaridar The Cable ta tattaro cewa 'yan kasuwa sun sayi Dala akan N1,600 kuma sun sayar a kan N1,620/$ wanda ya barsu da 'yar riba.
Wannan na nufin 'yan kasuwar sun samu ribar N20 kan kowacce Dala da aka yi musayarta a kasuwar hada-hadar kudin gwamnati.
Rahotanni sun nuna an yi musayar Naira a farashin da bai haura N1,620 ba kuma bai gaza N1,500 ba kan kowace Dala.
Darajar Naira ta kara faduwa
A wani labarin kuma kimar kudin Najeriya ta kara faduwar yayin da aka canza ta a kan N1,466.31 ga kowacce Dala a kasuwar musayar kudi.
Kasuwar hada-hadar musayar kudin ƙasashen ketare ta tabbatar da tashin Dala a tsakanin ranar Alhamis da Juma'a, inda farashin canjin ya karu da N40.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng