JAMB Ta Jero Sunayen Fitattun Jami'o'i 5 da Ake Zargin Su Na Aikata Babban Laifi a Najeriya
- Hukumar JAMB ta koka kan yadda wasu jami'o'i a Najeriya ke ci gaba da bayar da gurbin karatu ba bisa ƙa'ida ba
- Shugaban JAMB na ƙasa, Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana sunayen wasu jami'o'i biyar da ake zargi da bada haramtaccen gurbi
- Oloyede ya ce gwamnatin tarayya ta yafewa kusan mutum miliyan ɗaya da aka gano sun samu gurbin karatu ba bisa ƙa'ida ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu a Najeriya (JAMB) ta zargi wasu jami'o'i da bayar da gurbin karatu ba bisa ƙa'ida ba.
Shugaban hukumar JAMB na kasa, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya yi wannan zargin a wurin taron tsare-tsaren bada guraben karatu a Abuja ranar Alhamis.
JAMB ta fallasa sunayen jami'o'i 5
Ishaq Oloyede ya bayyana sunayen wasu jami'o'i da suka gano ana bayar da takardar admishin ta haramtacciyar hanya, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Makarantun da ya ambaci sunayensu sun hada da Jami’ar Najeriya, Nsukka (UNN), Jami’ar Abuja (UNIABUJA).
Sai kuma jami'ar tafi da gidanka watau Open University (NOUN), Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) da Jami’ar Jihar Delta (DELSU).
Taron wanda JAMB ta shirya ya samu halartar masu ruwa da tsaki a fannin bayar da guraben shiga manyan makarantun gaba da sakandire a ƙasar nan.
Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da shugabannin jami'o'i (VCs) da magatarkardansu, shugabannin kwalejojin fasaha da na kwalejojin ilimi.
JAMB: Gwamnati ta yafewa mutum miliyan 1
Farfesa Oloyede ya ce gwamnatin tarayya ta ɗagawa ɗalibai kusan miliyan ɗaya ƙafa waɗanda ake zargin sun shiga makarantun ba bisa ka'ida ba.
Ya ce ma'aikatar ilimi ta haƙura ta yafewa dukkan waɗanda suka samu gurbin karatu ta haramtacciyar hanya a tsakanin 2017 zuwa 2020.
Sai dai Farfesa Oloyede ya ce duk da hakan, wasu jami'o'i da manyan makarantu ba su daina aikata wannan babbban laifi da ya saɓawa doka ba, rahoton Leadership.
Ya ce daga cikin miliyan daya da aka yafe wa, mutum 600 kacal JAMB ta iya yi wa rijistar zuwa yanzu “saboda galibi ba su cancanta ba kwata-kwata.”
Ɗalibai 13 sun yiwa JAMB kaca kaca
A wani rahoton kuma Hukumar JAMB ya bayyana sunayen ɗaliban da suka ci maki mafi yawa a jarabawar share fagen shiga jami'a ta bana 2024.
Shugaban JAMB na kasa, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya sanar da sunayen ɗaliban a wurin taron majalisar gudanarwa ta hukumar a Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng