Zanga Zanga Ta Samu Babban Koma Baya, an Saka Sabanin Kabilanci a Cikin Tafiyar
- Kungiyar yan ƙabilar Ibo ta nuna fargabar kan shirin zanga zanga da ake yi a faɗin Najeriya saboda tsadar rayuwa da ake fuskanta
- Kungiyar Ọhanaeze Ndigbo ta yi kira na musamman ga yan kabilar Ibo da ke zaune a Arewa kan kaucewa zanga zangar da ake shirin yi a Agusta
- Ohaneze ta bayyana dalilai kan abin da yasa ta yi kira na musamman ga mutanenta a wannan karon musamman lura da abin da ya faru a baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Kungiyar yan kabilar Ibo a Najeriya ta dauki matakin da zai kawo koma baya ga shirin zanga zanga da matasa ke yi a Najeriya.
Kungiyar ta bukaci ƴaƴanta su kauracewa zanga zangar a sassa daban-daban na tarayyar Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar Ọhanaeze Ndigbo ta bayyana dalilai kan maganar da ta yi ga ƴaƴanta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ohanaeze ta yi kira kan zanga zanga
Kungiyar Ọhanaeze Ndigboe ta kabilar Ibo a Najeriya ta yi kira ga yan kungiyar da ke Arewacin Najeriya kan cewa su nisanci tarayya cikin zanga zangar da ake shirin yi.
Haka zalika kungiyar ta umurci ƴaƴanta a kudu maso yammacin Najeriya su dauki matakin kin fita zanga zanga.
Mazi Okechukwu Isiguzoro ne ya fitar da sanarwar ga ƴaƴanta kungiyar a ranar Talata da ta wuce, rahoton Punch.
Dalilin kiran Ohanaeze kan zanga zanga
Mazi Okechukwu Isiguzoro ya ce sun dauki matakin ne duba da yadda aka samu matsaloli a kan zanga zanga a tarihi.
Jagoran yan kabilar Ibon ya ce a shekarar 1978 an yi zanga zangar 'Ali Must Go' inda aka rika cutar da mutanensu.
Ya kuma kara da cewa an samu wasu zanga zanga da aka yi a baya wanda an cutar da yan kabilar Ibo saboda haka ne suka dauki mataki a wannan karon.
Zanga zanga: AYCF ta shawarci matasa
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Arewa Youth Consultative Forum (AYCF) ta yi kira na musamman ga matasa da ke shirin fita zanga zanga a Najeriya.
Kungiyar ta ba matasan shawara kan yadda ya kamata zanga zangar ta kasance domin kaucewa barkewar rikici da sace sace a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng