Tinubu Ya Yi wa Ƴan Kwadago Alƙawari 1 Bayan Amincewa da Albashin N70,000 a Aso Villa

Tinubu Ya Yi wa Ƴan Kwadago Alƙawari 1 Bayan Amincewa da Albashin N70,000 a Aso Villa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tura kudirin sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 zuwa majalisar tarayya a makon gobe
  • Mai bai shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka bayan cimma matsaya da ƴan kwadago
  • Bola Tinubu ya gana da ƴan kwadago a fadar shugaban ƙasa ranar Alhamis kuma sun ƙarƙare batun sabon mafi ƙarancin albashi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - A ranar Talata mai zuwa kudirin sabon mafi ƙarancin albashi zai isa majalisar tarayya bayan cimma matsaya a taron da ya gudana jiya Alhamis a Abuja.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da ƴan kwadago sun amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a taron da suka yi a Villa.

Kara karanta wannan

Satar Akuya ta jawo matar aure ta buga wa mijinta gatari, ya mutu nan take

Tinubu da shugabannin NLC da TUC.
Ranar Talata kudirin sabon mafi karancin albashi zai isa majalisa Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

An yanke albashin akalla N70, 000 a Najeriya

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, wannan adadin zai maye gurbin N30,000 wanda a doka wa'adinsa ya mutu tun a ranar 18 ga watan Afrilu, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba ku manta ba kwamitin aka kafa a watan Janairu ya mika alkaluma daban-daban ga shugaban kasa biyo bayan saɓani tsakanin mambobin kwamitin.

Yayin da tawagar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu suka yi tayin N62,000, kungiyoyin kwadago sun bukaci N250,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙaranci.

This Day ta ce a zaman da suka yi jiya Alhamis, Tinubu da ƴan kwadagon sun amince N70,000 ta zama sabon mafi ƙarancin albashin da za a biya ma'aikata a Najeriya

Yaushe Tinubu zai kai kudirin majalisa?

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya tabbatar da cewa za a miƙa kudirin sabon albashin ga majalisa zuwa Talata.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya zama na farko a Arewa da ya amince zai fara biyan ma'aikata N70,000

A kalamansa, ya ce:

"Ranar Talata kudirin sabon mafi ƙarancin albashi zai isa majalisa, shugaba Tinubu ya faɗawa ƴan kwadago a taron da suka yi cewa zai shirya komai zuwa Talata."

Wani ma'aikacin gwamnatin tarayya, Aliyu Nura, ya shaidawa Legit Hausa cewa ƙarin zai ragewa ma'aikata wasu abubuwan amma ba zai ɗauki nauyin iyali a wata ba.

"Ni ina ganin wannan sabon mafi ƙarancin albashin ba yabo ba fallasa, zai ɗan rage wasu abubuwan amma ba zai ɗauki mai iyali ba a wata."
"Muna fatan kada a ɗauki dogon lokaci kafin fara aiwatarwa domin ma'aikata na buƙatar duk abin da zai ɗan rage masu halin da ake ciki ko ɗan ya yake," in ji shi.

Gwamna ya musanta biyan albashin N80,000

A wani rahoton kuma Gwamnatin Ribas ta musanta labarin da ke bayyana cewa za ta biya sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jiha da kananan hukumomi.

Gwamna Siminalayi Fubara ya ce babu inda gwamnatinsa ta ayyana aniyar biyan N80,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262