"Ban Ce Zan Biya N80,000 ba," Gwamna ya Musanta Rahoton Zai Yi Karin Albashi

"Ban Ce Zan Biya N80,000 ba," Gwamna ya Musanta Rahoton Zai Yi Karin Albashi

  • Gwamnatin Ribas ta musanta labarin da ke bayyana cewa za ta biya sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jiha da kananan hukumomi
  • Gwamna Siminalayi Fubara ya ce babu inda gwamnatinsa ta ayyana aniyar biyan N80,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikata
  • Gwamnatin ta cikin sanarwa dauke da sa hannun sakataren yada labaran jihar, Nelson Chukwudi ta ce za ta bayyana matsayarta nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Rivers - Gwamnatin jihar Ribas ta musanta rahoton cewa za ta yi wa ma'aikata jihar sabon mafi karancin albashi.

Gwamna Siminalayi Fubara ne ya musanta labarin, inda ya ce gwamnati ba ta ce za ta biya N80,000 ga ma'aikatan jihar ba.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, NLC ta turawa majalisa gargadin tsaida ayyuka cak na kwanaki 30

Sir Siminalayi Fubara
Gwamnatin Ribas ta musanta rahoton biyan N80,000 mafi karancin albashi Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa rahotanni sun karade Ribas kan cewar gwamnati za ta biya ma'aikatan jiha da na kananan hukumomi N80,000 a matsayin mafi karancin albashi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati za ta bayyana matsayarta

Gwamnatin jihar Ribas ta ce nan gaba za ta sanar da matsayarta kan batun mafi karancin albashi, kamar yadda PM News ta wallafa.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren yada labaran gwamnatin jihar, Nelson Chukwudi.

"Ku guji yada labaran karya," Gwamnan Ribas

Gwamnatin jihar Ribas ta shawarci jama'a da su daina yada labaran karya ko wallafa shi, a daidai lokacin da ta ce rahoton za ta biya sabon albashi ba gaskiya ba ne, Vanguard ta wallafa.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta yi martani kan labarin cewa za ta biya sabon mafi karancin albashi ne saboda illar labaran karya da tasirinsa a zukatan ma'aikatan jihar.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da cin kwakwa, gwamna zai ba ma'aikata N45,000 domin rage raɗaɗin kunci

Tinubu ya yanke sabon mafi karancin albashi

A baya mun kawo labarin cewa gwamnatin tarayya ta yanke sabon mafi karancin albashi da za ta rika bawa ma'aikatan kasar nan bayan doguwar fafutuka.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yanke N70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi bayan fafutukar kungiyoyin kwadago na biyan N250,000 a baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.