Kano: Sarki Sanusi II Ya Koka Kan Halin Kunci da Ake Ciki, Ya Yabawa Gwamnatin Abba

Kano: Sarki Sanusi II Ya Koka Kan Halin Kunci da Ake Ciki, Ya Yabawa Gwamnatin Abba

  • Sarki Muhammadu Sanusi II ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan raba takin zamani ga al'ummar jihar baki daya
  • Sanusi II ya nuna damuwa kan halin kunci da ake ciki a yanzu musamman tsadar kayan masarufi inda shawarci masu hali
  • Wannan na zuwa ne yayin da gwamnan ya kaddamar da rabon taki zaman domin ci gaba da gudanar da ayyukan noma

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya koka kan halin kunci da ake fama da shi a fadin Najeriya baki daya.

Muhammadu Sanusi II ya godewa Gwamna Abba Kabir game da raba takin zamani kyauta ga manoma a fadin jihar baki daya.

Kara karanta wannan

Uba Sani ya ba da umarnin a zane Dan Bilki Kwamanda? Gwamnatin Kaduna ta magantu

Sanusi ya yabawa Gwamna Abba Kabir, ya koka kan halin kunci da ake ciki
Sarki Sanusi II ya yabawa Abba Kabir kan rabon takin zamani. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Abba Kabir Yusuf.
Asali: UGC

Kano: Sanusi II ya yabawa Gwamna Abba

Basaraken ya fadi haka a cikin wani faifan bidiyon da hadimin gwamnan Kano, Abdullahi I Ibrahim ya wallafa a shafin X a yau Alhamsi 18 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin bidiyon Sanusi II ya bukaci masu hannu da shuni su ci gaba da taimakawa manoma da takin zamani a jihar.

Ya ce hakan zai taimaka wurin samar da amfanin gona tare da rage tsadar kayan masarufi musamman na abinci.

Muhammadu Sanusi II ya koka kan halin kunci

"Mai girma Gwamna kamar yadda muke fada dazu, a yau mun samu takardu daga hakimai a kasar Garko, suna kokawa kan takin zamani, ashe wannan taki za a raba ne kyauta."
"Wannan shi ne abin da ya kamata, hukuma kullum ta mai da hankali kan damuwar al'umma."

Kara karanta wannan

Ndume: Daurawa ya nuna fargaba kan gwamnatin Tinubu, ya fadi illar haka gare su

"Taki yana da muhimmanci wurin yawaitar kayan abinci da kuma rage tsadar farashin kaya a cikin al'umma."
"Muna yawan samun korafi daga hakimai cewa kullum abinci kara tsada yake yi har ta kai wani sai dai a yanka masa rabin tattasai ya siya saboda tsada."

- Muhammadu Sanusi II

Dan Agundi ya caccaki maido Sanusi II

A wani labarin, kun ji cewa Aminu Babba Dan Agundi ya caccaki matakin mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarauta.

Dan Agundi ya ce Rabiu Kwankwaso ya tafka babban kuskure tun farko bayan mayar da Sanusi II kan karagar sarauta.

Ya ce Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya cancanci zama sarki saboda mahaifinsa jinin sarauta ne, haka bangaren mahaifiyarsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.