Zanga Zanga: Gwamnan Gombe Ya Fadi Abin da Jami’an Tsaro Za Su Yiwa Masu Zuga Matasa
- Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya gargadi matasa kan shirin shiga zanga zanga da ake ƙoƙarin yi
- Hakan na zuwa ne bayan gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi gargadi ga matasa kan zanga zanga a jiya
- Legit ta tattauna da wani matashi a jihar Gombe mai suna Muhammad Ibrahim domin jin yadda ya dauki maganar gwamnan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya dauki zafi kan maganar fita zanga zanga.
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya gargadi matasa kamar yadda Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi a jiya Laraba.
Legit ta tattaro muku abin da gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya fada ne a cikin wani bidiyo da Adamu A. Babale Makera ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zanga zanga: Gwamna ya shawarci matasa
Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya shawarci matasa kan su kauracewa zanga zanga.
Alhaji Inuwa Yahaya ya ce ka da matasa su yarda wani sheɗani ya zuga su wajen yin zanga-zanga a Najeriya.
Gwamnan jihar Gombe ya soki zanga zanga
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa zanga zanga ba abin da za ta jawo sai cutar da matasan da suke ƙoƙarin yin ta.
Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya ya kara da cewa zanga zanga za ta cutar da iyayen matasan dama Najeriya baki daya.
Zanga zanga: Za a yi maganin mayaudara
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce zuga matasa da ake su fito zanga zanga tamkar yaki ne da ya shafi kowa da kowa a Najeriya har da shugabanni.
Saboda haka gwamna Inuwa Yahaya ya ce matasa su zauna a gida, jami'an tsaro kuma za su yi maganin duk wani mayaudari da ya fito kan hanya.
Legit ta tattauna da Muhammad Ibrahim
Wani matashi a jihar Gombe, Muhammad Ibrahim ya bayyanawa Legit cewa maganar da gwamnan ya yi ta kama hankalinsa.
Ya ce tun a karon farko ma ba shi da niyyar fita zanga zanga kuma abin da gwamna Inuwa ya fada ya karfafesa.
Zanga zanga: Minista ya gargadi matasa
A wani rahoton, kun ji cewa ministan ayyuka, David Umahi ya ce bai kamata mazauna Kudu maso Gabas su tsunduma zanga-zanga ba.
Rahotanni sun nuna cewa ministan ayyuka ya bayyana haka ne a taron kaddamar da aikin titi a Abaliki da ke jihar Ebonyi a jiya Laraba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng