Jira Ya Ƙare, Shugaba Tinubu Zai Sanar da Adadin Sabon Mafi Ƙarancin Albashi a Najeriya
- Mai yiwuwa shugaban ƙasa, Bola Ahned Tinubu ya sanar da sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata yau Alhamais, 18 ga watan Yuli
- Wannan na zuwa ne bayan Bola Tinubu ya buƙaci majalisa ta ƙara makudan kudi a kasafin kuɗin 2024 saboda ƙarin albashin da za a yi
- Ana sa ran duk wani jira ya ƙare, Tinubu na iya bayyana adadin bayan ganawa da ƴan kwadago a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na iya sanar da adadin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya yau Alhamis, 18 ga watan Yuli, 2024.
Ana tsammanin za a bayyana sabon albashin ne a lokacin da shugaba Tinubu da ƴan kwadago suka koma teburin tattaunawa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Rahoton Independent ya nuna cewa a taron da suka yi na ƙarshe, Bola Tinubu ya ce ba dole sai an jira bayan shekaru biyar kafin a sake duba mafi ƙarancin albashi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, ya kamata a ce duk bayan shekara biyu zuwa uku a sake komawa teburin tattaunawa kan albashin ma'aikatan ƙasar nan.
Tinubu ya buƙaci ƙarin N6.2trn a kasafin 2024
Ranar Laraba, 17 ga watan Yuli, 2024, Bola Tinubu ya buƙaci majalisar dattawa ta ƙara N6.2trn a kasafin kuɗin 2024.
Shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti ta Tsakiya), ya ce kara kuɗin kasafin ya zama dole saboda saboda mafi ƙarancin albashi.
A lokacin da yake gabatar da kudirin jiya Laraba, Sanata Bamidele ya ce bayan ƙarin albashi, za a yi amfani da kudin wajen yin wasu ayyuka da tun farko ba a sa su a kasafin ba.
Bugu da ƙari, ana sa ran yau Bola Tinubu da wakilan ƙungiyoyin kwadago za su ƙarƙare batun ƙarin albashin a taron da aka tsara gudanarwa a Villa, Punch ta ruwaito.
Gwamnonin PDP sun faɗi matsayarsu
Kuna da labarin Gwamnonin jam'iyyar PDP sun bayyana goyon bayan buƙatar NLC na ƙarin mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya.
A wata sanarwa da kungiyar gwamnonin ta fitar bayan taro a Enugu, ta buƙaci a yi la'akari da ƙarfin arzikin gwamnatoci kafin yanke adadin ƙarin.
Asali: Legit.ng