Matasan Arewa Sun Fice Daga Shiga Zanga Zanga Kan Gwamnatin Tinubu, Sun Bayyana Dalili

Matasan Arewa Sun Fice Daga Shiga Zanga Zanga Kan Gwamnatin Tinubu, Sun Bayyana Dalili

  • Wasu ɗalibai daga gamayyar ƙungiyar CNYS sun janye daga shiga cikin zanga-zangar da ake shirin gudanarwa a faɗin ƙasar nan
  • Ɗaliban sun bayyana cewa sun ɗauki matakin fasa shiga cikin zanga-zangar ne saboda ba su san masu shirya ta ba
  • Sun nuna damuwa kan cewa zanga-zangar da ake shirin yi ka iya kawo naƙasu ga harkokin karatun da suke yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wasu ɗalibai na gamayyar ƙungiyar CNYS sun sanar da janyewarsu daga zanga-zangar da aka shirya yi a faɗin ƙasar nan domin matsalar yunwa da taɓarɓarewar tattalin arziƙi.

Shugaban ƙungiyar ɗaliban jihar Kano (NAKS), Kwamared Jibrin Sani Bello ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kano.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya ba 'yan Najeriya muhimmiyar shawara ana shirin fara zanga zanga

Matasan Arewa sun fasa zanga-zanga
Matasan Arewa sun fasa shiga zanga-zanga kan gwamnatin Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Meyasa matasan su ka fasa zanga-zangar?

Jibrin Sani Bello ya bayyana cewa janyewar ta samo asali ne daga damuwar cewa ba a san ko su waye masu shirya zanga-zangar ba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗaliban sun yi zargin cewa akwai masu bayar da kuɗi domin yin amfani da masu shirya zanga-zangar, wanda hakan ya sanya suka janye.

Ɗaliban sun jaddada cewa zanga-zanga kan kawo cikas ga harkokin ilimi, wanda hakan na iya yin illa ga karatunsu, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Yayin da suka amince da ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta a ƙasar nan, sun yi gargadin a guji ta'azzara lamarin ta hanyar zanga-zangar da ba ta dace ba.

"Shirye-shiryen zanga-zangar sun yi nisa, amma bayan mun yi tunani da shawarwari, bai kamata ɗaliban Najeriya su shiga zanga-zangar ba saboda rashin sanin masu shiryata."

Kara karanta wannan

Sukar Shugaba Tinubu ta jawo sanatan Arewa na fuskantar barazana a zaben 2027

"Mun fahimci halin matsin tattalin arziƙin da ƴan Najeriya ke ciki, amma mun yi amanna cewa shiga cikin zanga-zangar ka iya haifar da abin da za a yi dana sani."

- Kwamared Jibrin Sani Bello

Karanta wasu labaran kan zanga-zanga

Zulum ya ba da shawara kan zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ba al'ummar Borno da ƴan Najeriya baki ɗaya shawara kan zanga-zangar da ake shirin gudanarwa.

Gwamnan na jihar Borno ya buƙace su da su guji shiga zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan a watan Agustan 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng