Bola Tinubu Ya Sake Ɗauko Mace, Ya Naɗa Ta a Shirgegen Mukami a Gwamnatin Tarayya
- Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Didi Esther Walson-Jack a matsayin sabuwar shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya
- Esher za ta maye gurbin shugabar ma'aikatan, Dr Folasade Yemi-Esan wanda za ta yi ritaya daga aiki a ranar 13 ga watan Agusta
- A sanarwar da ya fitar, mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya ce Esther za ta kama aiki ne ranar 14 ga Agusta, 2024
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Misis Didi Esther Walson-Jack, OON, a matsayin sabuwar shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya.
Bola Tinubu ya bayyana cewa sabon naɗin zai fara aiki ne daga ranar 14 ga watan Agusta, 2024.
Bola Tinubu ya nada Walson-Jack
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 17 ga watan Yuli, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dada Olusegun, mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin soshiyal midiya ya wallafa sanarwar naɗin a shafinsa na X watau Twitter.
Sanarwar ta ce Misis Walson-Jack ta zama babbar sakatariya a 2017 kuma ta yi aiki a ma'aikatu daban-daban na tarayya gabanin a naɗa ta a wannan muƙami.
Ta kuma ƙara da cewa wadda aka naɗa za ta maye gurbin shugabar ma'aikatan tarayya ta yanzu, Dr Folasade Yemi-Esan, wacce za ta yi ritaya ranar 13 ga Agusta.
Shugaba Tinubu ya godewa mai barin gado
Sanarwar ta ce:
"Wacce aka nada za ta gaji shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya mai ci, Dr. Folasade Yemi-Esan, CFR, wacce za ta yi ritaya a ranar 13 ga Agusta, 2024.
“Shugaba Tinubu ya gode wa shugabar ma’aikata mai barin gado bisa aikin da ta yi, kana ya buƙaci sabuwar shugabar ta sauke nauyin da ya rataya a wuyanta cikin gaskiya da rikon amana.
"Ya kuma roƙi shugabar ma'aikata mai jiran gado ta bi dokoki da ƙa'idojin aiki wajen sauke nauyin da ya hau kanta."
APC ta kare Tinubu kan rabon muƙamai
A wani rahoton kuma APC mai mulki a Najeriya ta fito ta kare shugaban ƙasa Bola Tinubu kan rabon muƙaman da yake yi a gwamnatinsa.
Jam'iyyar APC ta bayyana cewa Shugaba Tinubu na ƙoƙarin ganin ya yi adalci domin ganin kowane yanki ya samu muƙami mai gwabi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng