An Kama Ɗan Gwamna Zulum da Zargin Hallaka Wani a Gidan Gala a Indiya? Gaskiya Ta Fito
- Yayin da ake yada jita-jitar cewa ɗan Gwamna Babagana Zulum ya hallaka wani a Indiya, gwamnatin jihar ta fayyace gaskiya
- Gwamnatin ta ƙaryata labarin da ake yadawa cewa yaron ya hallaka wani ɗan Indiya a gidan Gala bayan samun hatsaniya
- Wannan na zuwa ne bayan yada kabarin cewa ana zargin cafke ɗan gwamnan da kisan wani a Indiya kan mata a gidan Gala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ta yi martani kan zargin ɗan Gwamna Babagana Zulum da hallaka wani a Indiya.
Gwamnatin ta ƙaryata jita-jitar inda ta ce ba a cafke matashin ba kuma babu abin da ya aikata na laifi.
Zulum: Gwamnati ta ƙaryata zargin ɗan Gwamna
Hadimin gwamnan a bangaren kafar sadarwa ta zamani, Abdurrahman Ahmed Bundi shi ya bayyana a yau Laraba 17 ga watan Yulin 2024, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bundi ya ce babu kamshin gaskiya a maganar kuma ba a tasa keyar yaron zuwa gidan gyaran hali ba kamar yadda ake yaɗawa, Daily Trust ta tattaro.
Ya ƙaryata rade-radin cewa Zulum ya tafi kasar Indiya domin shawo kan lamarin inda ya ce gwamnan ya tafi kasar Masar ne domin halartar taro.
Gwamnatin Borno ta yi gargadi kan jita-jita
"Mun samu labaran da ake yadawa cewa an kama ɗan Gwamna Zulum kan zargin kashe wani ɗan ƙasar Indiya."
"An buga labarin a kafar 'Nairaland cewa Zulum ya tafi Indiya domin shawo kan lamarin."
"Muna mai tabbatar da cewa 'Nairaland' da sauran kafafen sadarwa sun buga labarin ba tare da tantancewa ba."
"Muna tabbatarwa al'umma cewa babu wani ɗan Zulum da aka kama ko kuma ya aikata wani laifi makamancin haka."
- Abdurrahman Ahmed Bundi
Gwamna Zulum zai iya kai kara kotu
Gwamnatin jihar ta bukaci wadanda suka yada labarin su sauke tare da ba Zulum da iyalansa hakuri cikin awanni 24 ko su fuskanci shari'a.
Wannan na zuwa ne bayan yada jita-jitar cewa ɗan gwamnan ya hallaka wani a Indiya a gidan Gala da ake zargin mace ce ta hada rigimar.
Zulum ya shawarci matasa kan zanga-zanga
Kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ba al'ummar Borno da ƴan Najeriya baki ɗaya shawara kan zanga-zangar da ake shirin yi.
Gwamnan na Borno ya buƙace su da su guji shiga zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan a farkon watan Agustan 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng