"Tinubu na Kokari, Kar ku Shiga Zanga Zanga," Minista Ya Lallabi Jama'a

"Tinubu na Kokari, Kar ku Shiga Zanga Zanga," Minista Ya Lallabi Jama'a

  • Ministan ayyuka, David Umahi ya ce bai kamata mazauna Kudu maso Gabas su tsunduma zanga-zanga ba
  • Ministan ya bayyana haka ne a taron kaddamar da aikin titi a Abaliki da ke jihar Ebonyi a ranar Larabar nan
  • Sanata Umahi ya ce sun tattauna da gwamnonin yankin Kudu maso Gabas, kuma ba za a yi zanga-zanga ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ebonyi- Ministan ayyuka, David Umahi ya shawarci mazauna Kudu maso Gabas da kar su amsa kiran zanga-zanga da ake shirya wa a kasar nan. Ministan ya roki al'ummar yankin da ya fito ne a garin Abaliki a Larabar nan yayin kaddamar da aikin titi a Abaliki.

Kara karanta wannan

Shugaban APC Abdullahi Ganduje ya fadi dalilin karuwar cin hanci da rashawa

Governor David Nweze Umahi
Ministan ayyuka ya roki matasan Kudu maso Gabas su guji zanga-zanga Hoto: Governor David Nweze Umahi
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa cewa Ministan ya ce Bola Tinubu na iya kokarinsa wajen magance halin da 'yan kasa su ka shiga.

Umahi ya nemi a taimaka wa Tinubu

Ministan ayyuka, David Umahi ya ce shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauki tsauraran matakan da ya dauka ne domin gyara kasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan, wanda ke kokarin hana matasa fita zanga-zanga ya ce Tinubu na bakin kokarinsa wajen rage matsin da ake fuskanta, Daily Post ta wallafa.

Umahi ya ce abin da ya kamata shi ne 'yan Najeriya su taya Tinubu da addu'a domin cimma kyawawan manufofinsa.

"Ba za ayi zanga zanga a Ebonyi ba,"

Ministan ayyuka a gwamnatin Bola Tinubu, Mista David Umahi ya ce ba za a yi zanga-zanga a Kudu maso Gabas ba.

Umahi ya ce tuni ya gana da gwamnonin jihar Ebonyi da na sauran jihohin Kudu maso Gabas, kuma an cimma matsaya.

Kara karanta wannan

Masoyan Tinubu za su dauki mataki kan Sanata Ali Ndume bisa sukar shugaban kasa

Ya ce mazauna Kudu maso Gabas na ganin kyakkyawan canji da karuwar ayyuka a yankunansu tun bayan bawan mulkin Tinubu.

Zanga-zanga: Gwamna ya bayar da shawarar

A wani labarin kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya shawarci jama'ar jihar da kar su yi zanga-zanga da ake shirin yi a watan gobe

Shawarar ta zo a gabar da matasan kasar nan ke shirin zanga-zangar gama gari a kan tsadar rayuwa da ake zargin kudure-kuduren gwamnati da jawo wa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.