Gwamna Radda Ya Kafa Tarihi a Katsina, Ya Yi Abin da Aka Dade Ba a Yi Ba

Gwamna Radda Ya Kafa Tarihi a Katsina, Ya Yi Abin da Aka Dade Ba a Yi Ba

  • Mai girma Gwamnan jihar Katsina ya miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Malam Faruk Lawal Jobe
  • Gwamna Dikko Umaru Radda ya miƙa ragamar mulkin domin tafiya hutun wata ɗaya bayan majalisar dokokin jihar ta amince da hakan
  • Wannan dai shi ne karo na biyu a tarihin mulkin siyasa a jihar Katsina da wani gwamna mai ci ya miƙa ragamar mulki ga mataimakinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina Dikko Umaru Radda ya miƙawa mataimakinsa, Faruk Lawal Jobe ragamar mulkin jihar.

Gwamna Radda ya miƙa masa mulkin ne domin tafiya hutun wata ɗaya wanda zai fara daga ranar Alhamis, 18 ga watan Yulin 2024.

Gwamna Radda ya tafi hutu a Katsina
Gwamna Radda ya mika ragamar mulki ga mataimakinsa Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Gwamna Dikko Radda ya miƙa mulkin Katsina

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai ƙazamin hari, sun kashe basarake mai martaba da ɗansa a Arewa

Mataimakin gwamnan, Malam Faruk Lawal Jobe zai cigaba da jan ragamar jihar a matsayin muƙaddashin gwamna a tsawon wannan lokacin, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kakakin majalisar dokokin jihar, Nasiru Yahaya Daura ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar na ranar Talata, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

An amince da tafiya hutun gwamnan ne biyo bayan wasiƙar da aka aikawa kakakin majalisar, wacce mai tsawatarwa na majalisar Alhaji Ibrahim Dikko ya karanta a yayin zaman.

A cikin wasiƙar, Gwamna Radda ya kawo misali da sashe na 190 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima), wanda ya ba majalisun jihohi ikon amincewa da irin wannan buƙata daga ɓangaren zartarwa.

Gwamnan Katsina, Radda ya kafa tarihi

Wannan shi ne karo na biyu a tarihin mulkin siyasa a jihar Katsina da wani gwamna mai ci ke neman amincewar majalisa domin tafiya hutu da miƙa mulki ga mataimakinsa.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamna ya tsokano rigima, ya faɗi gwamnan PDP da ya yi yunƙurin kashe shi

Karon farko da hakan ya faru, ya faru ne a lokacin mulkin marigayi Gwamna Umaru Musa Yar’adua.

Haka kuma a lokacin da Gwamna Radda yake a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Charanchi, shi ne shugaban ƙaramar hukuma ɗaya tilo a jihar Katsina da ya miƙa ragamar mulki ga mataimakinsa.

Tafiya hutun bai kamata ba

Legit Hausa ta tuntuɓi wani mazaunin jihar Katsina mai suna Zaharaddeen Hamisu wanda ya nuna cewa tafiya hutun da gwamnan zai yi sam ba dace ba.

"A ra'ayina, ina ganin cewa bai kamata Gwamna Dikko Umar Radda ya tafi wannan hutu ba a daidai wannan lokaci da 'yan ƙasa ciki har da 'yan jihar Katsina ke fama da matsin rayuwa ba."
"Babban abinda ya fi kamatuwa a gareshi shi ne haɗa gwiwa da sauran takwarorinsa gwamnoni wajen samawa al'umma mafita daga wannan ƙangi da ake ciki."

- Zahraddeen Hamisu

Gwamna Radda ya nemi alfarma wajen Katsinawa

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya zama na farko a Arewa da ya amince zai fara biyan ma'aikata N70,000

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya buƙaci al'ummar jihar da su yi addu'o'i domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro.

Gwamna Dikko Radda ya buƙaci al'ummar musulmin su roƙi Allah maɗaukakin Sarki ya kawo ƙarshen matsalar da ta ƙi ci, ta ƙi cinyewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng