Gwamna Ya Dauki Matakin Inganta Wutar Lantarki a Kano, Abba Zai Kashe N7.1bn

Gwamna Ya Dauki Matakin Inganta Wutar Lantarki a Kano, Abba Zai Kashe N7.1bn

  • A zaman majalisar zartarwar jihar Kano na 16, gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauki matakin da zai kawo ingantar wutar lantarki a jihar
  • Hakan na zuwa ne bayan samun tangarɗa da ake yawan yi a harkokin wutar lantarki wanda ke shafar sana'o'i da ayyukan al'umma
  • Haka zalika gwamnan ya amince da ma'aikatar KASITDA wanda za a tafi mataki na gaba domin mayar da ita doka a jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamantin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta dauki matakin inganta wutar lantarki a fadin jihar Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauki matakin ne a zaman majalisar zartarwar jihar Kano da ya gudana a yau Laraba.

Kara karanta wannan

Abba Kabir Yusuf ya fara muhimman ayyuka 10 da za su shafi talakawa a Kano

Abba Kabir
Gwamnatin Kano za ta inganta lantarki. Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanan da gwamna Abba Kabir ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kano: Abba zai gyara harkar wuta

A yau Laraba gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da sayen sababbin na'urorin trasifoma 500.

Gwamnatin jihar za ta kashe makudan kudi har sama da N7bn wajen sayen sababbin na'urorin.

A ina za a raba na'urorin lantarkin?

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da cewa za a raba na'urorin ne a sassa daban-daban cikin kananan hukumomin jihar Kano 44.

Ana sa ran matakin da gwamnatin ta dauka zai kawo sauki ga matsalolin lantarki da ake fama da su a jihar.

Abba ya amice da kafa ma'aikatar KASITDA

Haka zalika a zaman majalisar zartarwar, gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da kafa ma'aikatar cigaban fasahar zamani ta KASITDA.

Kara karanta wannan

Kofar Mata: Abba Kabir, Kwankwaso sun tura sako ga kwamishina bayan iftila'in gobara

A yanzu haka za a saurari majalisar dokokin jihar Kano ta mayar da kudurin samar da ma'aikatar KASITDA doka mai zaman kanta.

Abba ya biya yan fansho a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya ƙaddamar da shirin biyan kuɗin giratuti kashi na biyu a mulkinsa.

Gwamnan ya ƙaddamar da biyan kuɗaɗen waɗanda sun kai Naira biliyan 5 daga shekarar 2016 zuwa 2019.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng