Kotu Ta Umarci Sake Shari’a Kan Rigimar Masarauta, Ta Ce an Tafka Kuskure

Kotu Ta Umarci Sake Shari’a Kan Rigimar Masarauta, Ta Ce an Tafka Kuskure

  • Kotun Daukaka Kara ta ba da umarnin sake duba a kan shari'ar da aka yi game da dambarwar sarauta a jihar Ondo
  • Kotun ta umarci sake shari'ar da ake kalubalantar Sarkin Ile-Oluji, Oba Oluwole Julius Olufaderin da ke jihar
  • Tun farko, iyalan Jimoko da ke ikirarin gadar sarautar sun maka Oba Julius a kotu inda suke kalubalantar zamansa sarki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ondo - Kotun Daukaka Kara a Akure da ke jihar Ondo ta umarci sake zama kan shari'ar masarauta.

Kotun ta umarci sake duba shari'ar da ake yi kan kalubantar Sarkin Ile Oluji, Oba Oluwole Julius a karamar hukumar Ile Oluji/Okeigbo.

Kotu ta ba da sabon umarni kan dambarwar sarauta
Kotun Daukaka Kara ta umarci sake shari'ar neman tsige basarake a jihar Ondo. Hoto: Legit.
Asali: Original

Ondo: Hukuncin kotu kan rigimar sarauta

Kara karanta wannan

Kwamishinan Kano ya tsallake rijiya da baya, iyalansa 3 sun mutu a gobara

Mai Shari'a Olabasi Omoleye ya dauki wannan mataki a yau Laraba 17 ga watan Yulin 2024, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin da sauran alkalan da suka hada da Oziakpono Oho da T. Y Bashir sun tabbatar da cewa an tafka kuskure yayin shari'ar.

Kotun ta ce ta dauki matakin ne bayan Babbar Kotun jihar da ke Akure ta yi fatali da korafin inda ta ce dole a sake shari'ar a wani kotun daban.

Ondo: Musabbabin rigimar sarauta tsakanin iyalai

Idan ba a manta ba, an nada Oba Julius ne a matsayin sarkin Ilu-Oluji a shekarar 2018 bayan mutuwar tsohon sarkin da ke kan kujerar.

Sai dai Iyalan Jimoko da ke ikirarin gadar sarautar sun maka Oba Julius a kotu inda suke kalubalantar kasancewarsa sarki.

A cikin korafin da suka yi ta bakin lauyansu, Otunba Olayinka Bolanle sun yi fatali da sarkin inda suka ce ba ya daga cikin masu gadon sarautar.

Kara karanta wannan

Ondo: Dan takarar gwamna ya fadi mafi karancin albashin da zai biya idan ya ci zabe

Dan Agundi ya soki Kwankwaso kan masarautu

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Dawaki Babba, Baffa Dan Agundi ya yi magana kan masarautun jihar Kano.

Dan Agundi ya soki Sanata Rabiu Kwankwaso inda ya ce ya tafka babban kuskure tun farko wurin dawo da Sanusi II.

Ya ce wanda yafi dacewa da sarautar Kano shi ne Aminu Ado Bayero saboda shi ne dan Sarki kuma jikan Sarki a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.