'Yan Sanda Sun Samu Nasara Kan Miyagun 'Yan Bindiga a Jihar Katsina
- Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta bayyana nasarar da jami'anta suka samu kan ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Kankara
- Rundunar ta ce jami'an ƴan sandan tare da haɗin gwiwar jami'an rundunar KSWC da ƴan banga sun hallaka wani ɗan bindiga guda ɗaya
- Jami'an tsaron sun kuma ƙwato bindiga ƙirar AK47 guda ɗaya daga hannun ƴan bindigan bayan sun yi artabau
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta ce ta samu nasara kan ƴan bindiga a jihar.
Rundunar ta ce jami'anta sun yi nasarar kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne a gundumar Ketare da ke ƙaramar hukumar Kankara.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq-Aliyu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun yi nasara kan ƴan bindiga
Kakakin ƴan sandan ya kuma bayyana cewa an ƙwato bindiga ƙirar AK47 guda ɗaya daga hannun ƴan bindigan, rahoton Daily Post ya tabbatar.
Ya bayyana cewa jami'an ƴan sandan sun yi bata-kashi da ƴan bindigan ne bayan sun ji labarin cewa sun kai hari ɗauke da bindigu a ƙauyen Gidan Dan Ali da ke ƙaramar hukumar Kankara.
ASP Abubakar Sadiq ya ci gaba da cewa bayan samun rahoton, DPO na ƴan sandan Kankara ya tura tawagar ƴan sanda da jami'an rundunar KSWC da ƴan banga zuwa ƙauyen.
Jawabin rundunar 'yan sanda
"Tawagar ta samu nasarar bin sahun ƴan bindigan zuwa ƙauyen Bulunkuza, inda suka yi musayar wuta wanda hakan ya sanya suka tsere ba tare da cimma manufarsu ba."
"A yayin da ake duba wajen da aka yi artabun, an gano gawar wani da ake zargin ɗan bindiga ne da kuma bindiga ƙirar AK47 guda ɗaya."
- ASP Abubakar Sadiq-Aliyu
Karanta wasu labaran kan ƴan bindiga
- 'Yan bindiga sun yiwa jami'an tsaro kwantan ɓauna, an rasa rayuka a Katsina
- Katsina: 'Yan bindiga sun turo saƙon bidiyon mutanen da suka sace a Maidabino
- "Akwai ma'aikatanmu da ke aiki da 'yan ta'adda," Shugaban jami'a a Katsina
Ƴan bindiga sun saki mahaifiyar Rarara
A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen mawaƙin siyasar nan, Dauda Adamu Kahutu Rarara ya bayyana cewa ƴan bindiga sun saki mahaifiyarsa bayan kwashe wajen mako biyu tsare.
Mawakin ya kuma miƙa godiya ta musamman ga abokan sana'arsa da ma masoyansa baki daya bisa irin kulawar da suka nuna masa da taya shi alhinin sace mahaifiyarsa da aka yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng